mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

DAME ZAMU KAFA DALILI KAN WANDA YAKE FADIN CEWA DALILAN DA MUKE KAWO WA KAN MAFI CANCANTUWAR AHLIL-BAITI A.S DALILI NE MARA KARFI

Salamu Alaikum masu sabani damu suna bijire mana da dalilai guda biyu
Na farko: jumlar riwayoyin da muke kafa dalili da su kan marja’iyyar Ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata a garesu wadanda suka kasance riwayoyi ne daga hanyar Ahlus-suuna dama basu da inganci kwata-kwata musammam ma hadisul Saklaini da ya zo da sigar (littafin Allah da tsatsona matukar kuka yi riko da su ba zaku taba bata ba bayana har abada) kune fa kuke sanya sharadin ilimi da yakini cikin sanin Imami.

 

Salamu Alaikum masu sabani damu suna bijire mana da dalilai guda biyu

Na farko: jumlar riwayoyin da muke kafa dalili da su kan marja’iyyar Ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata a garesu wadanda suka kasance riwayoyi ne daga hanyar Ahlus-suuna dama basu da inganci kwata-kwata musammam ma hadisul Saklaini da ya zo da sigar (littafin Allah da tsatsona matukar kuka yi riko da su ba zaku taba bata ba bayana har abada) kune fa kuke sanya sharadin ilimi da yakini cikin sanin Imami.

Na biyu: hadisan da kuke rawaitowa daga Imamanku (a.s) wadanda kuke raya cewa sun wadatar daku daga sauran riwayoyi cikin tabbatar da mafi cancantuwar mazhabarku da kuke raya cewa ingantattu ne suna tukewa ne zuwa ga Imam Bakir da Sadik (a.s) basa kaiwa ga Manzon Allah (s.a.w) hukuncinsu daya da hadisi mursali wanda kuma ba hujja bane, bari dai ko da ma ace Imamanku sunyi bayani karara da cewa suna rawaito su daga kakansu (s.a.w) hakan ba zai amfanar ba cikin galibin lokuta saboda basa Ambato hanyoyin da suka rawaito daga Manzon Allah (s.a.w) tayi hanya ce da ba a dogara da ita cikin ilimin hadisi.

Yaya zamu basu amsa kan wannan ishkali?

Allah ya saka muku da alheri.

 

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Kadai dai muna kafa musu dalili da shaida da litattafansu bawai da cewa bamu da dalilai ba a wurinmu da zamu yi riko da su, bari dai domin bin tsarin tattaunawa tareda su daga babin jidali da abinda yafi kyawu sai mu ke lazimta musu abinda suka lazimtawa kawukansu daga abinda muke kawowa daga hadisai da suke hujja a wurinsu sai mu kafa musu hujja da su bawai hujja bane a kawukanmu mu muna da namu kebantattun hanyoyin da suke tabbatar da cancantuwar Ahlil-baiti Amincin Allah ya kara tabbata a garesu cikin da’a da soyayya dole addininmu ya kasance daga gidan Manzo (s.a.w) sune siradi mikakke neman shiriya daga waninsu daidai karkata da bata.

sannan riwayarmu ba ta kasance mai yankakken isnadi ba, lallai ya tabbata a gurinmu cewa duk abinda Imamai biyu Albakir da Sadik (a.s) suka fada Magana ce da Manzon Allah kamar yanda yake maganar Kur’ani mai girma bas a fadin abinda ya sabawa maganar Manzon Allah (s.a.w) ko fadin Allah Azza wa Jalla sakamakon imaninmu da gaskiyarsu da ma’asumancinsu na zati bai cutarwa don basu ambaci isnadin da yake tsakaninsu da kakansu Manzon Allah(s.a.w) dukkaninmu a wurinmu haske guda daya hakika ce daya muhammadiya da take gudana rahama ga dukkanin talikai, dalilansa duk sun gurbata, abinda muke fadi shine gaskiya, muna godiya ga Allah wanda ya sanya mu daga wadanda suke riko da wilayar Sarkin Muminai

da yayansa ma’asumai tsarkaka, gaskiya zata bayyanar da Ahalinta duk yanda zamani yakai da tsayi, ku jira lokaci ni ma ina tareda ku daga cikin masu jiran lokaci Allah ya dawwamar daku cikin alheri.

 

Tarihi: [2019/11/5]     Ziyara: [475]

Tura tambaya