mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

SHIN SUNAYE SUNA DA TASIRI CIKIN LAFIYA SHIN ALJANI YANA IYA SATA

Salamu Alaikum. Ina da wani dan’uwa ya kai shekaru biyu da haihuwa sai dai kowanne lokaci yana fama da rashin lafiya da dumamar jiki da ciwon Asma cikin godiyar Allah cutar tasa ba mai daukar dogon lokaci ba ce… sunansa Ali,
Wasu mutane suna cewa wai in canja sunansa wai ta iya yiwuwa sunan Ali ya zama yayi masa karfi da yaw aba zai oiya dauka ba, gashi mu muna riko da wannan suna mai albarka muna alfahari da shi.

 

 

Salamu Alaikum. Ina da wani dan’uwa ya kai shekaru biyu da haihuwa sai dai kowanne lokaci yana fama da rashin lafiya da dumamar jiki da ciwon Asma cikin godiyar Allah cutar tasa ba mai daukar dogon lokaci ba ce… sunansa Ali,

Wasu mutane suna cewa wai in canja sunansa wai ta iya yiwuwa sunan Ali ya zama yayi masa karfi da yaw aba zai oiya dauka ba, gashi mu muna riko da wannan suna mai albarka muna alfahari da shi.

Tambaya anan shine.. shin suna yana da tasiri kan lafiya kamar yanda mutane ke rayaw? Shin dole sai mun canja sunan? Idan ya zama dole sai mun canja sunan to wanne suna ne ya fi dacewa da shi?

Matsala da biyu: mu fama da matsalar bacewar kudi a cikin gidanmu musammam cikin daki babata kuma ba zamu iya cewa ga wanda ya sata ba da ace barawo yake sadadowa ya sace ai da ya sace zinariyar da take cikin dakin da tufafi da sauran kayayyaki ko kuma da mung a sawunsa, shin aljanu suna sat? wasu mutane sun gaya mana haka kuma babata ita fai fuskantar matsalar bacewar kudadenta ta kusa zautuwa duk sanda ta ajiye kudi bayan kwanaki biyu ko yini guda sai ta neme su sama da kasa ta rasa, ta yi sallar neman taimako (salatul istigasa bi Fatima)  domin gano kudaden sai a mafarki ta ga wata Mage tana ce mata wannan abinda kike cigiya sai ga na kudadena da suka bata cikin wata rufaffiyar kwarya kuma nag a dukkanin abinda na rasa watannin baya sai kwatsam na farka daga mafarki.

Yawancin lokacin kudaden suna bata yayin da na ajiye su a dakin babata na kan yi tambaya ince na fa ajiye su a dakin babata ne amma babu wanda yake gasgata ni sai nayi rantsuwa ba zan kara ajiyewa ba a dakin babata zan ajiye a wani dakin daban, dana ajiye babu wani abu da ya kara bata.

Tambaya anan shine shin Kenan aljanu suna sata? Idan da gaske suna yi to menen mafita?

 

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Hadisi mai daraja ya zo yana bayyana cewa sunaye suna saukowa daga sama, haka zalika daga cikin sunaye masu albarka akwai sunan (Aliyu) lallai an tsago shi daga sunan Allah Jalla Jalaluhu sannan duk gidan da a cikinsa akwai mai suna Ali haka mai suna Muhammad da Fatima da Hassan da Husaini lallai Allah yana albarkantakarsa yana kuma kore talauci daga barinsa  za kuma su ga wadata, duk wanda sunansa ya kasance Ali to yayi alfahari da shi, lallai ya kasance daga sunayen A’imma (a.s) guda hudu na farkonsu Sarkin Muminai Aliyu Ibn Abu Dalib (a.s) sannan ga Imam Zainul Abidin Aliy Ibn Husaini (a.s) sannan Imam Aliyu Ibn Musa Arrida (a.s) sai Imam Aliyu Ibn Muhammad Alhadi (a.s) idan kuma son canja sunan to ku jingina masa Muhammad sai dinga kiransa Muhammad Aliyu, ya zo cikin Du’a’u Tawwasul

 
( يامحمد ياعلي ياعلي يامحمد اكفياني فإنكما كافيان وانصراني فإنكما ناصران)

Ya Muhammad ya Ali ya Ali ya Muhammad ko isar mini lallai ku masu isarwa ni ku tallafeni lallai ku masu tallafawa ne.

Ka roki Allah da wannan suna mai albarka da yaron ya kasance cikin kariyar Allah da kulawarsa ya kubuta daga ya warke da sunan Allah ya Shafi mai warkarwa ya Mu’afi mai bada lafiya da yardar Allah ta’ala.

amma dangane da satar Aljani da wai cewa aljani ko yana sata ko kuma ba ya yi, to bisa la’akari da shi a matsayin mukallafi domin daga cikin aljanu akwai wadanda sukai Imani da Allah da Manzonsa haka daga cikinsu akwai wadanda suka kafirce kamar yanda ya zo cikin suratu Jinni, sannan Kafiran cikin aljanu da fasikansu basu da banbanci da sauran mutane suma suna aikata ayyukan sabo, sannan daga cikin sabo akwai sata, babu kokwanto idan satar ta kasance daga garesu, sai dai abin tambaya anan shin aljani yana yiwa dan’uwansa aljani sata kamar yanda a zahiri kamar yanda mutane suke yiwa junansu sata, ko kuma yana sacewa mutum ne? to wannan ya bukatar dogon bincike, shin Aljani yana samun wannan dama da iko? A zahiri dai bai da misalin wannan damar da har zai yi wa mutane sata daga wadanda suke ba jinsinsa ba

Allah ne masani.

Sai dai cewa akwai shaidu da suke nuna cewa Aljani yana cutar da mutum, sai dai cewa shin yana cutar da shi ta hanyar sata? Wannan ya bukatar dalili da bincike na ilimi da fa’idantuwa da haka ta hanyar dalilan shari’a daga ayoyin da riwayoyi ni kuma zuwan yanzu hakan bai tabbata a gareni ba,

Allah ne masani.

 

Tarihi: [2019/11/3]     Ziyara: [2112]

Tura tambaya