mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

HIRZI GUDA BAKWAI WANDA AKE DANGANTA SHI GA ANNABI SULAIMAN A.S

Salamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu
Samahatus Assayid na ji kunce Aljani bai da samuwa babu shi kwata-kwata wahami kawai , sai dai cewa cikin littafin Iksirul Da’awat akwai wata kissa da ta zo daga Annabi Sulaiman (a.s) da cewa ya hadu da Aljani ya tashi sama kan dardumarsa sannan sun tattauna da juna sannan Annabi Sulaiman (a.s) ya sanya wadannan Hirzozi guda bakwai, kaka haka ta faru?

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai]

Raddina da rashin laminta ta bai kasance cikin Kubrar dalilil ba kadai dai ya kasance cikin Sugrar dalil.

Bayani: ni banyi inkarin asalin samuwar Aljani ba tareda sunayensu da kungiyoyinsu daga cikinsu akwai tabi’u da tabi’atu kadai dai bayani shine yawancin abinda ke yawo a bakunan mutanen gari ni ina daukarsa wahami da shirme da sakarci kadai, shi wahami idan yayi yawa sai yayi galaba kan ilimi sai mai yin wahami ya dauka cewa wahaminsa ilimi ne, sai ya dinga suranta cewa a jikinsa akwai wata Aljana da take manne da shi da dai abinda yayi kama da haka, babban abinda zai ishe ka shaida kan karyar hakan shine idan ka ga mutum ya raya cewa wai akwai Aljani a jikinsa da yake damfare da shi kace masa zaka cire masa wannan Aljana ta hanyar yanke hannuwansa guda biyu ka dauko wuka ka nuna masa fa kai da gaske yanke hannun Aljanar zaka yi nan take zaka ji yace maka ai tuni Aljanar ta fita daga jikinmu da zarar ya ga kaifaffen karfe ya nufo sai kaji suna cewa ai ta fita ai ta fita, wannan dalili da yake bayyana cewa babu koma tareda su sai hiyali da wahamin cikin kwakwale, sabid ahaka ne nake ganin wahami ne kawai bawai ina inkarin asalin samuwar Aljani da Aljana bane.

Wurin ubangiji ake neman taimako.

Tarihi: [2019/12/3]     Ziyara: [479]

Tura tambaya