mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wanne aikin ibada ne mafi muhimmacin a kwanakin tattakin Arba’in

Salamu Alaikum.

Allah ya girmama ladanku da namu, ya kuma saka muku da alheri kan gudummawar da kuke bayarwa

Cikin yardar Allah mun daura damarar niyyar ziyarar Arba’in din Imam Husaini amincin Allah ya kara tabbata a gareshi

Salamu Alaikum.

Allah ya girmama ladanku da namu, ya kuma saka muku da alheri kan gudummawar da kuke bayarwa

Cikin yardar Allah mun daura damarar niyyar ziyarar Arba’in din Imam Husaini amincin Allah ya kara tabbata a gareshi. Sabida haka ne nake son kuyi mini nasiha da wani aikin ibada da zai shagaltar da tunanina da hankalina da ruhina cikin tunawa da Allah da zanyi tanadinsa in amfana daga gareshi musammam lokacin da na isa Kabarin Imam Husaini (a.s), wacce ibada ce mafi muhimmanci a ake yinta a wadannan tsarkakan wurare, ta kaka zan rabauta ga kaiwa zuwa ga haske?Allah ya saka muku da mafificin alheri ya baku lada.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Na karanta wasikarka mai daraja da aka aiko, sai dai baki daya abinda yale da muhimmanci cikin rayuwar Mumini bayan sanin Allah a farkon lokaci shine kada ya sake ya aikata sabo da kuma iklasi shin mai kasani daga iklasi lallai ya zo daga Sarkin Muminai aminci Allah ya tabbata a gareshi yana cewa: (da iklasi ake samun kubuta) daga shaidanin makiyi na waje da kuma na badini a boye haka daga zunubai da miyagun akidu, sannan (kayi iklasi zaka samu komai) ma’ana zaka samu duk abinda kake so za kuma ka kai duk inda kake son zuwa, kadai shi iklasi yafi dandakuwa daga silin gashi yafi takobi kaifi babu mai samun rabauta da shi sai mai babban rabo, saboda haka ka rungumi nafiloli bayan sauke farillai.

Allah mai bada taimako. 

Tarihi: [2020/11/11]     Ziyara: [357]

Tura tambaya