mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Shin zai yiwu ga imam Mahadi ya hadu d muminai cikin gaiba kubra cikin surar saurayi wani karon kuma ya zo da surar tsoho tukuf.


Salamu alaikum samahatus sayyid
Sayyid ina da tambaya wacce ban samu gamsasshiyar amsa kanta ba shi ne wai shin kuwa zai yiwu imam Mahadi ya hadu da muminai cikin sura da shigar saurayi a wani karon kuma ya zo da surar tsoho tukuf tare da furfura. Akwai wata riwaya a cikin littafin biharul-anwar da aka rawaito daga imam Sadik (as) cikin riwayar yana cewa:(lallai Allah ya baiwa halliru daga karfi da zai iya surantuwa da dukkanin surar da yaso surantuwa da ita) wannan ga halliru kenan yaya ga imam Mahadi (af) mene ne martaninku Allah ya saka muku da alheri.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Allah ya shiryar da mu da ku zuwa ga abin da cikinsa akwai alheri da farin ciki, sannan ka sani lallai annabi haka wasiyyi suna bangaren `yan`adamtaka na tsarin rayuwa a doron kasa kamar sauran mutane, suna ci suna sha suna yawo a kasuwanni (lallai shi ba komai bane face mutum misalinku) sannan suna da janibin malkutiya da ya shallake mada da abubuwan da ta lazimta daga zamani da bigire da wasunsu, lallai shi daga gaibu yake da abubuwan da basu da jikkuna kamar misalin hankula tsantsa kamar mala’iku, a wannan lokaci bisa la’akari da janibin malakutiyya zai iya yiwuwa ya shakkalu da shakalai daban daban sai dai cewa hakan na daga ababen yabawa kyawawa, kamar misalin shakkaluwar Jibrilu (as) cikin saukar da wahayi ga manzon Allah (s.a.w) da surori daban-daban da surar dahiyatu kalabi kyakkyawan saurayi a madina kamar yadda a ka nakalto ya kuma shahara, a wannan lokaci zai iya yiwuwa ga ma’asumi daga babin mu’ujiza da masalaha da hikimar Allah ya shakkala fagage daban-daban ya kasance saurayi sai kuma bayan dan wani lokaci ya zo a tsoho tukuf haka ma ya kara zuwa a saurayi a wani lokacin.

Ta fuskanin yiwuwa a zati a cikin duniyar tabbatuwa babu wata matsala cikin haka, zai wanzu ta fuskanin yiwuwa afkuwar yana hakan bukatuwa zuwa ga dalili tabbatar da hakan idan anyi sa’a hakan ya tabbata sai mu tafi kansa in kuma ba samu dalili ba sai mu barshi a bigiren yiwuwa har sai sanda muka samu dalili kamar masana falsafa da hikima ke cewa:

 (كل ما يقرع سمعك فذره في بقعة الإمكان حتى تجد له دليلاً)

Dukkanin abin da ke kwankwasar kunnanka ka kyale shi cikin bigiren yiwuwa har sai ka samu dalili kansa.

Lallai yadda batun yake mu `ya`yan dalili ne dukkanin inda ya juya nan muke juyawa, amma abin da ka ambata dangane da shugabanmu imamin zamaninmu ruhina da ruhin talikai fansa ga kurar takunsa dubun amincin Allah ya kara tabbata gare shi, lallai hakan na iya yiwuwa gare shi da yiwuwar zati, kadai zai wanzu yana jiran dalili cikin yiwuwar afkuwa wannan ne ban samu dalili kansa ba Allah ne masani
Tarihi: [2018/1/13]     Ziyara: [677]

Tura tambaya