mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Mene ne ma'anar ya Zakiyu ya tsarkakakke daga dukkanin aibu da tsarkakarsa

Salam Alaikum Sayyid mai daraja da girma ni daga kasar Iraki na ke daga cikin jumalar abin da ya zo daga daya daga cikin Arifai daga malamanmu masu daraja shi ne ya Zakiyu ya tsarkakakke daga dukkan aibu da tsarkakarsa.
Muna rokon sayyid ya taimaka mana da Karin bayani .

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Allah matsarkaki mai tsarki tsarkakke cikin zatinsa da siffarsa da cikin ayyukansa, ma'anar tsarkakuwa da tsarkaka shi ne cewa shi tsarkakakke ne daga dukkan tawaya da aibu da mummuna domin dukkan wanda ya kasance haka zai zama mumkini, shi kuma Allah samuwara wajibi ce ga zatinsa shi mawadaci ne abin nufi da bukata, shi tsarkakakke ne matsarkaki , kamar yanda yake cikin mukamin siffofi da ayyukan sa hakama ya kasance tsarkakakke. Idan ya kasance tsarkakakkke cikin zatin sa to lallai tsarkakakke ne cikin ayyuka da zantukansa, lallai tsantsar kyawu daga gareshi kyawu yake gangarowa, lallai shine kyawu yana kuma son kyawu yana kuma son kyakkywawa shine tsarkakakke daga dukkanin tawaya da aibu.

 

Tarihi: [2018/7/5]     Ziyara: [1614]

Tura tambaya