mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Mene ne sabubban rashin amsa addu’a?

Me yasa tare da cewa ina yawan addu’a amma duk da haka ba a amsa mini addu’a ta?

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai

 

Lallai Allah a cikin kowanne hali yana amsa addu’a saboda shi ne da kansa yayi alƙawarin hakan kuma shi ba zai taɓa sabawa abinda yayi alƙawari ba, sai dai cewa kawai wani lokacin mune bama kiyaye sharuɗɗan addu’a kamar yadda aka ambace su a mahallinsu cikin litattafan sunnoni da ladubba, kamar yadda ya zo cikin littafin uddatu da’i, kamar yadda da za ka kirashi daidai lokacin da cikinka ke ɗauke da lomar abincin haramun lallai Allah ba zai amsa ba a wannan lokaci, wannan kenan da farko, na biyu kuma amsa addu’a wani abu ne daban sannan kuma samun biyan bukatarka wani abu ne daban lallai amsa addu’a yanada martabobi guda biyar koma fiye da haka mafi ƙanƙantarsu shine biya maka buƙatarka, idan ba haka lallai akwai wasu amsawar Allah da suka fi girmama daga biya maka buƙata, tareda haka kada ka ce Allah baya amsa mini addu’a ta.

Allah ne abin neman taimako.   

Tarihi: [2018/2/5]     Ziyara: [748]

Tura tambaya