mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Na gaji daga halin da `dana abin tausayi yake ciki ta yadda `kananan yara ke masa isgili basa kwadayin yin wasa tare da shi ina rokon samahatus-sayyid ya nusantar da ni zuwa ga warwarewa ina sa ran Allah zai yaye mini wannan matsala


Na gaji daga halin da `dana abin tausayi yake ciki ta yadda `kananan yara ke masa isgili basa kwadayin yin wasa tare da shi ina rokon samahatus-sayyid ya nusantar da ni zuwa ga warwarewa ina sa ran Allah zai yaye mini wannan matsala.

amincin Allah ya tabbata ga bawansa na gari sayyid adil-alawi Allah ya dawwamar maka da fairorinsa
sayyid lallai ni `daya daga cikin `ya`yanku ne daga garin kadif saudiya ina rubuto muku wannan wasika tawa ba wai ina nufin kai karar Allah ba Allah ya tsarkaka daga haka, bari dai don neman taimako da fuskantarwa daga gareku cikin wasu al’amura guda biyu:
na farko: shi ne cewa Allah ya azurta ni da samun `da na kuma ra`da masa suna da sunan muhammad sai dai cewa wasu matsaloli sunyi kacibus dani tare da haihuwar wannan `da na wa mai albarka ta yadda mahaifiyarsa ta haifeshi yana da watanni takwas da daukar cikinsa sai ya zamanto yayi jinkiri cikin koyon zama da koyon rarrafe haka cikin koyon tafiya, mun godewa Allah mun samu damar ziyartar imam rida (as) ya kuma fara tafiya cikin albarkar imam rida (as) yanzu kam ba ya magana sai da wasu `yan kididdigaggun kalmomi, na kai shi wajen likita amma hakan bai bada fa’ida ba, na karanta ziyarar ashura na lazimceta fiye da shekaru hudu sai dai cewa har ya zuwa yanzu nan bai yin magana sosai, na kuma jarraba hadisin kisa’i da karanta du’a’u tawassul har sai da na fara dimauta cikin lamarina, na yi zaton cewa dukkanin hanyoyi fa sun kulle gareni, yayin da na ke jin hakan sai na nufi imam husaini (as) da mahaifinsa sarkin muminai aliyu bn abu dalib (as) sa raina ko Allah zai sanya kulawarsu ta tattaro da ni, na yi matukar gajiya daga halin da `da na abin tausasawa ke ciki ta yadda yara `kanana ke yawan yi masa isgili ina fatan samahatus sayyid zai nusantar da ni zuwa ga abinda zai warware wannan matsala sa raina Allah zai raba ni da wannan matsaloli.
Wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu

 

بسم الله الرحمن الرحیم

Da sunan Allah mai rahama mai ji kai

Shi mumini yana cikin jarrabawa wannan tabbataccen abu ne daga nassoshin addini da akidarmu cikin makarantar ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata gare su, sai dai cewa daga jarrabawa da ibtila’i akwai abin da ke tafiya ta hanyar magancewa ko yin sadaka ko karanta addu’a da ziyarori daga cikinsu akwai abin da ke kasancewa daga hukuncin Allah da `kaddararsa to irin wannan wajibi ga mumini ya rungumi hakuri a kansa saboda irin wannan ibtila’i na kaddara sila ne zuwa ga kamalarsa da kamalar wadanda suke kewaye da shi, kamar misalin mara lafiya da aka jarrabce shi da cutar da aka ga za gano maganinta, idan ya zama mun masa bakin kokarinmu cikin nemar masa waraka mukai sauke dukkanin abinda ya wajaba kanmu daga kaishi wajen likitoci da cibiyoyin kula da marasa lafiya mu kayi addu’o’i mukayi bakance mukayi salloli da zikirai sannan sai ya zama dukkanin abin da  mu kayi bai amfanar da shi ba, a wannan lokaci sai mu tsallaka zuwa kashi na biyu daga bala’i da jarrabawa shi ne jarrabawar da ya zama wajibi a rungumi hakuri cikinta sannan rungumar hakuri cikin jarrabawa yana daga alamomin wadanda sukai imani sukai aiki nagari, tabbas suna daga cikin wadanda Allah ya yabe su  

 (وتواصوا بالصبر)

Sukai wasicci da hakuri.

Kowanne dayansu yana wasiyya ga `dan’uwansa da ya yi hakuri da hukuncin Allah da kaddararsa da bala’insa da jarrabawarsa, matukar dai kai bakin kokarinka wajen neman magani ga mara lafiya amma hakan bai amfane shi, babu abinda ya rage face rungumar hakuri irin hakurin masu godiya kan musibar da ta same su, kamar yadda yake cikin sujjadar ziyarar ashura, sai kai hakuri ka godewa Allah kan wannan jarrabawa da bala’i domin ita jarrabawar dalili kan cewa Allah yana sonka kamar yadda ya zo cikin riwaya: mafi yawaitar soyayyarku shi ne wanda aka fi yawaita masa bala’i mafi kusancinku wurin Allah shi ne mafi yawan bala’i. Kamar yadda muke samun annabawa da wasiyyansu da waliyyai da salihai da ire iren misalsalansu sune suka fi kowa tsanantar bala’i, ka da ka `debe tsammani daga rahamar Allah da jin kansa da farko sannan kayi hakuri ka kuma godewa Allah daga karshe, kayi bakin kokarinka ka kara dagewa karo na biyu cikin hakuri da godiyar Allah.

Allah ne abin neman taimako ina maka addu’a tare da `danka da alheri da samun lafiya, nima kada ku manta da ni cikin addu’arku.

Allah ya dawwamar da ku cikin alheri da lafiya

Allah ne abin neman taimako   

Tarihi: [2017/11/1]     Ziyara: [891]

Tura tambaya