mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wanene ya cewa Imam Hassan (as) Assalamu Alaika ya mai kaskantar da miminai

Shin abinda malaman tarihi suke fadi ya inganta wai Hajarul Addi (rd) ya je wajen Imam Hassan Almujtaba bayan sulhun da yayi tare da Mu’awiya, sai yace masa amincin Allah ya tabbata a gareka ya mai kaskantar da muminai?

Shin abinda malaman tarihi suke fadi ya inganta wai Hajarul Addi (rd) ya je wajen Imam Hassan Almujtaba bayan sulhun da yayi tare da Mu’awiya, sai yace masa amincin Allah ya tabbata a gareka ya mai kaskantar da muminai?

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Yanayin ya tsananta matuka a zamanin Imam Hassan Almujtaba (as) hakan ya bada gudummawa rikicewar al’amari ga wasu ba’arin shi’ar sa makusanta sai dai cikin godiyar Allah take gaskiya da hakika ta yaye garesu ta bayyana suka dawo kan shiriyar da suke.

Amsa daga ofishin Ayatullah Assayid Adil-Alawi

Imam Hassan (as) ya kasance zaune tare da mutane a kofar gidan sa, sai Sufyanu bn Laila ya wuce yace  Assalamu Alaika ya mai kaskantar muminai.

Sai Imam (as) yace: wa Alailka Salam ya Sufyanu! Sai Sufyanu ya sauka daga kan Rakumin sa ya dan tattaka ya daure Rakumin sa sannan ya zauna.

Sai Imam (as) yace masa me kace ya Sufyanu?

Yace: nace Assalamu Alaika ya mai kaskantar da muminai.

Sai Imam (as) yace: me ya kawo wannan Magana haka da ta gudana kan harshenka ?!

Sai yace: mahaifana fansarka, wallahi mun wayi gari kaskantattu tun ranar da kayi sulhu da Azzalumi ka sanya al’amuran mutane a hannun wannan `dan Hindu mai cin hanta, tareda cewa kama dubban mazaje da suka zare takubban sub a kuma sa fara yaki face sai ka fara, Allah zai tara maka al’amuran mutane.

Sai yace: ya Sufyanu! Mu Ahlil-baiti duk sanda gaskiya ta bayyana garemu muna aiki da ita, naji daga babana Ali (as) yana cewa: naji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: yini da darare ba zasu kare har al’amarin al’umma ya kasance a hannun wani mutum mai katon ciki yana cin abinci amma bai koshi, Allah bai kallon sa d akallon rahama, ba zai mutu ba har sai ya zamanto babu wani da zai yarda da shi daga mutanen sama, kuma mutanen kasa basa son sa, wannan shi ne Mu’awiya, ni kuma ina da yakini cewa Allah ya yi aiki da iradar sa.

Ka koma ka duba littafin Al’iktisas sh 82 fasalin Sufyanu bn Laila Alhamdani.   

Tarihi: [2019/6/4]     Ziyara: [520]

Tura tambaya