mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Menene cikakken yakini (yakinit tam)

Assalamu alaikum sayyid mai girma tareda rahamar Allah da albarkarsa gareka.
Sau da yawa-yawan lokuta muna karantawa muna saurare daga laccocinku ko kuma daga maganganun malaman addini masu daraja kai hatta cikin manya-manyan litattafai da rubututtukan sakafar muslunci da cewa daga abubuwan da suke Katanga da hana amfanuwar da yawa-yawan musulmi musammam ma shi’a daga kur’ani da ziyartar kaburburan a’imma tsarkaka da karatun zikirai ingantattu cikin biyan bukata da warkar da mara lafiya da neman bukata da abin da Allah yake yarduwa da shi ne sakamakon rashin cikakken yakini, da yawa-yawan mu daga cikin ni kaina a kebance ina fama da wannan matsalar, hakika ban san menene dalili ba shin rashin samun cikakken yakini ne kan al’amarin ko kuma wani abu ne daban, babbar matsalar ma kacokan shi ne ni ban san menene cikakken yakinin ba, shin shi ne shu’urin da muke ji a zuciya ko kuma wani ayyanannen yanayi ne na imani da yake samuwa yayin karanta kur’ani da zikirai, ko kuma wani yanayi ne mai hauhawa da yake danganewa da karfaffa da ibadoji na wajibi da na mustahabbi da mu’amaloli da aikata na halal dinsu da kauracewa haramun da nesantar sabo da zaikata zunubai….
Tambayata Allah ya saka muku da alherinsa anan shi ne ta kaka za mu samu cikakken yakini ko kuma wacce hanya ce za ta kaimu ga cikakken yakini domin samun amfana da kur’ani mai girma da ziyarar humbare makwantan a’imma tsarkaka da zikirai cikin biyan bukatu da warkewar marasa lafiya, Allah ya saka muku da mafi alherin sakamako
Amincin Allah da albarkatunsa su tabbata gareku.

Menene cikakken yakini (yakinit tam)

السلآم عليكم سيدنا الجليل ورحمة الله وبركاته...

Da sunan Allah mai raham mai jin kai

idan kana san ka san cewa shin sallarka ta samu karbuwa ko kum ba ta samu ba?

To daga cikin alamomin karbuwarta shi ne ita sallah dai ta kasance tana hana aikata alfasha da munkari, idan kaiwa sallar biyayya cikin umarninta da haninta to tabbas kai an karbi sallarka, amma idan mutum ya aikata zunubi bayan sallah to wannan alama ce ta cewa sallarsa ba ta karbu ba karbuwar tak’wa da kamala wacce take janyo kammaluwar mutum da dagawar darajarsa da dacewa cikin tafiyarsa da sulukinsa, kadai dai ana karba daga gare shi ingantacciya kawai wanda shi ne sauke taklifi da kuma cewa shi ba zai maimaita sallah ba. Wannan alama ce mai kyau don sanin yakini, shin bayan sallah zaka ji cewa sallarka tana hanaka kallon matar da bata halasta ka kalleta ba alal misali ko kuma shin sallar tana hanaka yin gulma ko saurarenta ko tarayya da wanda yake yin gulma hakika sauraren gulma yafi girma daga zunubin mai yin gulmar sau saba’in, idan har ba zaka iya kare wanda ake gulmarsa ba to abin da ya wajaba kanka shi ne  ka tashi daga majalisin da ake gulmar kada ka damu da zargin mai zargi cikin sha’anin Allah, wanda yake da yakini kan wuta ba zai taba jin kunya kan fadin gaskiya ba, lallai shi zunubi hakikaninsa da badininsa duk wutar jahannama ne, nesa-nesa ya aikata zunubi ba, kai zai kare kansa daga zunubi wannan shi ne abin da ake kira da (is’ma if’aliya) wanda take wajen waliyyan Allah da salihan bayi.

Mafi falalar al’amri shi ne ka samu yakini wanda shi ne barin aikata zunubai kananansu da manya har tsawon shekara guda a wannan lokaci da sannu zaka san yakini cikin zuciyarka tabbatattun abubuwa za su yaye gareka, daga wannan lokaci ka kuduri niyya barin aikata sabo da zunubi dukkaninsu ka fara da aibobin harshe kamar yadda malaman akhlak suka ambata kana iya komawa littafin jami’us sa’adat na malam naraki da mahajjatul baida’u  na faizul kashani don Karin bayani, sannan kayi aiki da abin da ya zo cikinsu  daga kyawawan dabi’u ka komawa risala amaliya ta wanda kake taklidi da shi, ka koma littafin aka’idul imamiyya ka yi aiki da abin da ya zo ciki a wannan lokaci zaka riski darajojin farko na yakini da farkon ilimin yakini sannan kai ta tsinkayar wadannan darajoji har zuwa masha’Allah  cikin hakkul yakini daya bayan daya zasu yi ta riskarka kamar misalin kwayar carbi idan damki kwaya daya ka jata ta biyu sai ta riskeka kai ta yin haka harka riski kwayar karshe,

WAJEN ALLAH MUKE NEMAN TAIMAKO

Tarihi: [2017/8/13]     Ziyara: [1343]

Tura tambaya