mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Ina fama da rashin samun kwanciyar hankali da rashin dacewa a rayuwance

Salamu Alaikum:
Ina da wasu ba’arin matsaloli ina son bayyana maka su da nusantar da su gareka Sayyid,
Tsawon lokacin ina fama da rashin samun tsayayyen tunani da rashin samun dacewa a rayuwa ta, na samu jinkiri da karatuna na jami’a ban samu shaidar kammala karatu har zuwa yanzu, dukkanin tsaraiku na da shekarunmu suke bai daya sun kammala karatu sun sami aikin yi sun yi aure, ni ko har yanzu ina nan ina ta fama da kaina da fada da son zuciyata, ban samu dacewa ba cikin karatuna, ban yi aure ba gashi kuma ina fama da yawan motsawar sha’awa, hakika na wayi gari komai na motsa ni,, ina bakin kokarina cikin kowanne lokaci wajen ganin na kasance mutumin kirki da yake taka tsantsan da kansa. Sai dai cewa lokaci zuwa lokaci ina afkawa cikin aikin haramun ina kallon abinda yake haramun, na ji ma cikin wannan hali, hakika ni ina sa’ayi da dukkanin bakin kokarina wajen ganin na kasance bawan Allah nagari kamar yanda Allah ke so yake kuma yarda, da’iman ina karanta tarihin bayin Allah nagargaru ina kuma bakin iyawata wajen ganin zamantowa irinsu ko kuma alal akalla in siffantu da su, sai dai cewa tare da haka kafata ba ta gushe ba tana zamewa lokaci zuwa lokaci… sakamakon abinda nake fama da shi daga matsaloli,, ina fatan ka shiryar da ni Sayyid masoyinmu zuwa ga abinda zai warware matsalolina, da izinin Allah zai aikata dukkanin abinda Sayyid ya umarce da aikatawa.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Wannan sa’ayi da fafutika da kake na daga cikin alamomin samun azurtarka a nan gaba, lallai yadda lamarin yake shi ne cikin wata rana da sannu zai kasance kusa zaka kubuta daga wadannan matsaloli daga zunubai ka rayu cikin rayuwa ma cike da nutsuwa daddada mai cike da farin ciki insha’Allah Ta’ala, saboda haka kada ka debe tsammani daga rahamar Allah lallai ita tana kusa, sannan ka wanzu cikin halin nadama da rarrawar ruhi domin kubuta daga sabo da zunubai lallai Allah yana son matashi mai fitunuwa ma’ana wanda yake aikata zunubai cikin gaggawa ya tuba ya kara maimaita haka har wata rana ya tuba ya bar aikatawa kwata-kwata.

Allah ne abin neman taimako.  

 


Tarihi: [2018/4/9]     Ziyara: [958]

Tura tambaya