Deprecated: __autoload() is deprecated, use spl_autoload_register() instead in /home/net25304/al-alawy.net/req_files/model/htmlpurifier-4.4.0/HTMLPurifier.autoload.php on line 17
MUNA BUKATAR KARIN BAYANI KAN WANNAN RIWAYAR
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

MUNA BUKATAR KARIN BAYANI KAN WANNAN RIWAYAR

daga Sa’ad Ibn Abu Kalaf daga Najamu daga Abu Jafar amincin Allah ya tabbata a gareshi yace: ya Najamu dukkanin ku kuna aljanna tareda mu sai dai cewa mai yafi muni da mutum daga cikinku ya shiga aljanna alhalin Allah ya keta alfarmar tsaraicinsa ya bayyanar da shi, yace raina fansarka yanzu hakan zai kasance sai yace: na’am matukar bai kare farjinsa da cikinsa ba.

Me wannan riwaya take nufi shin tana nufin Allah yana keta suturar bawansa sannan ya gafarta masa a lahira ya kuma shigar da shi aljanna, ta kaka haka zata kasance. ashe ba Allah ne ya suturta aibobi ba, ta kaka riwaya zata zo tana cewa tsaraicinsa ya bayyana, ta yaya zamu yi fahimta Allah yana suturta aibobi a kuma daidai wannan lokaci yana keta sutura yana bayyanar da aibobin bawa, saboda wai me wannan rowaya take bayani ne?

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ya zo cikin Du’a’ul Kumaili (ka gafarta zunuban da suke keta kariya) wannan na nuna cewa a lahira akwai zunubai da suke jawo kecewar sutura da kariya da kuma jawo tonen asiri, hakan na kasantuwa kan mutumin da yake biyewar sha’awe-sha’awe cikinsa da farjinsa daga abubuwan haramun , ita duniya ana rufi aibobi da tsaraici amma lahira gidan tonen silili ce, kowacce halitta ana tone aibobinta da asrarenta a can.

Allah ne mai suturtawa da bada kariya.

Tarihi: [2019/9/5]     Ziyara: [490]

Tura tambaya