mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Menene banbancin tsakanin makarantar Ilmul Kalam da makarantar Falsafa

Salam Alaikum.. maulana tambayar mu ta farko itace: meye banbanci tsakanin Falsafa da Kalam? Shin wajibi ne mutum yayi Imani da daya daga cikinsu? Saboda wasu suna cewa Falsafa daidai take da kumfar gasara bata da amfani wasu kuma suna cewa larura ce?

Tambaya ta biyu: shin aiki da ziyarar Ashura da du’au Ahad da Sabahi da wasunsu yana bukatar neman izini daga gareku? Allah ya saka muku da alherinsa

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Banbanci tsakaninsu yana kasancewa tareda la’akari da abinda aka dogara da shi daga dalili, alal misali wurin masana falsafa dalili shine hujjojin hankali, amma wurin malaman Kalam dalili shine hujjojin hankali tareda na nakali littafin Allah da sunnar tsarkakka, abinda yake wajibi shine sanin Allah matsarkaki da Imani da dayantarsa daga kowacce hanya ne hakan ya tabbatu, lallai ka sani kumfar gasara ba zata taba kai ka zuwa ga Allah ba, babu banbanci daga falsafa ne ko daga ilimin kalam ko aga kowanne ilimi ne.

Tanbayarka ta biyu: bai bukatar izini daga kowa, lallai su suna daga ayyukan mustahabbi a kankin kansu.

Wurin Allah muke neman taimako

Tarihi: [2019/3/27]     Ziyara: [669]

Tura tambaya