mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Shin rashin amincewar mahaifiya cikin aure yana zama sabawa iyaye

Salamu Alaikum ni budurwa ce na kai shekaru 42 amma banyi aure ba sakamakon ni nake kula mahaifiyata sakamakon da tsufa matuka kuma bata son ta ga nayi aure, shin yin aure na ba tare da lamintar ba zai zama sabawa iyaye Kenan kuma zai jawo fushin Allah kaina???

Ku fa’idantar dani Allah ya baku lada mai tarin yawa

Salamu Alaikum ni budurwa ce na kai shekaru 42 amma banyi aure ba sakamakon ni nake kula mahaifiyata sakamakon da tsufa matuka kuma bata son ta ga nayi aure, shin yin aure na ba tare da lamintar ba zai zama sabawa iyaye Kenan kuma zai jawo fushin Allah kaina???

Ku fa’idantar dani Allah ya baku lada mai tarin yawa.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Lamintar mahaifiya baya daga cikin sharadin ingancin aure, kuma saba mata a cikin bai jawo fushin Allah lallai shine mai jujjuya zukata da idanu da sannu zai samar miki yardar mahaifiyarki da ikonsa da ludufinsa madaukaki, kije kiyi auranki kawai Allah ya sanya albarka.

Allah ne abin neman taimako.

Tarihi: [2018/12/19]     Ziyara: [599]

Tura tambaya