mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Me nene hukuncin jihadi a bayanan ayatollah khamna’I da kuma ayatollah Sistani?

Assalamu alaikum
Na kasance ina da wata aqida akan jihadi domin kare hurumin musulunci, a ko ina, naga sayyid khamna’I yana goyan bayan zuwa jihadi kasar suriya, sai na daura wa kaina domin na je kare aqida ta, amma kuma da na duba fatawan sayyid Sistani banga yana nuna goyan bayan hakan ba. Wannan ya janyo na sami rudewa, don a yanzu haka bana taqlidi da kowanne a cikin su, domin duk san da na ke son zuwa jihadi sai a ke cewa sayyid Sistani ba ya goyon baya, amma innace kuma zanyi taqlidi da sayyid Khamna’I don na je jihadi a suriya ko Iraqi sai ace ai sayyid Sistani ya fi sani (أعلم).

Da sunan Allah me rahama me jin kai

Irin wannan tuniani kuskure ne, don haka muje mu ne mi wa nene yafi ilimi cikin maraji’ai ta hanya na shar’I wato hanyar da ta fi dacewa, duk wanda yafi ilimi ya tabbata maka duk wanda ya tabbata maka ya fi ilimi to dole ka bi duk abin da yace, ko ya goyi bayan a yi jihadi ko kuma be goyi baya ba, domin duk abin da ka aikata ko kukure ne shi ke da laifi in kuma daidai ne to dukan ku zaku samu lada.

Tarihi: [2016/10/16]     Ziyara: [1117]

Tura tambaya