mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Shin rashin yardar mahaifiya kan aure na iya zama sabawa iyaye


Salamu Alaikum
Ni budurwa ce da shekaruna suka kai 42 banyi aure ba sakamakon ni ce na ke kula da mahaifiya wacce tsufa ya riske ta sannan duk sanda na so yin aure sai ta ki yarda.
Shin idan nayi aure ba tare da yardar ba shin hakan zai zama sabawa iyaye kenan wanda zai jawo mini fushin Allah???
Ku fa’idantar damu Allah ya saka muku da gwaggwaban lada.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Yardar uwa ba sharadin bani cikin ingancin kulla aure tare da lazimcin aure sannan saba mata cikin hakan ba zai jawo fushin Allah matsarkaki madaukaki ba. Lallai shi Allah shi ne mai jujjuya zukata da sannu zai sanya mahaifiyarki yarda cikin kudirarsa da ludufinsa, saboda haka kawai kiyi aurenki mai albarka insha’ Allah Allah ne mai taimako.

Tarihi: [2018/1/8]     Ziyara: [758]

Tura tambaya