mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

MENE NE HUKUNCIN CINIKIN DA AKE BIYAN KUDADE A TSINTSINKE A RARRABE DA KARO GUDA BA

Salamu Alaikum
Daya daga cikin yan kasuwa yana sayar da nama sai dai cewa mu a namu yankin ba a biyan kudi take hannu, akwai wadanda suke biya a tsitstsinke da cak din banki, shin mai sayar da kaya zai iya kasa farashin kayansa zuwa kashi biyu alal misali wanda zai biya take hannu ya sayar masa da kilo daya a 500 wanda kuma zai dauka bashi 600 ya biya a rarrabe shin hakan ya halasta a shari’a

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Kasuwanci ya kasu zuwa kashi biyu: ba’ul nakadi cinikin kudi hannu, da kuma bai’ul nasi’ati: wanda cikinsa ake biyan kudi daga baya da ake sanya kayyadadden lokaci, kamar yanda a dabi’ance wurin mutane ba’ul nasi’ati yafi yawan farashi sakamakon lokacin da yake dauka kafin a biya ya halasta kuma ba a kirga shi daga cinikin riba, zai iya sayarwa da farashin dinare dari idan ya kasance kudi hannu idan kuma bashi ne nasi’ati dinare 150 alal misali, sai dia cewa zai karbi kudin bayan wata sannan an shardanta cewa abinda za a saya dole ya kasance bayyananne daga kowacce fuska daga haja da kudin kai harda mudda da aka kayyade sakamakon Annabi (s.a.w) ya yi hani kan bai’ul garari wanda aka jahilci wani bangare daga cikinsa daga bangarori  

Tarihi: [2019/11/3]     Ziyara: [549]

Tura tambaya