mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Lokaci cikin kulla auren mutu’a

Mun kulla auren mutu’a tsawon watanni shida sai dai cewa shi yana zaune wani gari nima ina zaune a wani gari daban babu abin ya afku tsakaninmu tareda cewa mun yi yarjejeniyya zai zo a bikin idi sai dai cewa mun samu sabani sakamakon kasantuwarsa mai yawan sauraren wake-waken zamani da kuma shan giya barasa kuma har zuwa yanzu yaki yafe mini ragowar lokacin da ya rage a cikin auren, mene ne ya zama wajibi na?

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ya zama wajibi gareki kiyi hakuri har zuwa lokacin da kuka yi yarjejeniya ya kare ma’ana wannan watanni shidan ai basu da yawa da sannu zasu kare kusa-kusa, matsaloli su kare sukau kowanne lokaci ki dinga kasantuwa cikin ido bude ki di nga taka tsatsan lallai shi mumini mutum ne mai kaifin basira da hangen nesa haka muminta ita take, wannan ya zama darasi mai kyawu ga gobenki nan gaba kada kim kara sakewa ki cilla kanki hannun wanda yake aikata haramun, lallai su mutanan banza abokan tarayyarsu mutanen banza, mutanen kirki abokanan tarayyarsu `yan’uwansu mutanen kirki.

Allah ne mai karewa shi ne kuma abin neman taimako.

 

Tarihi: [2017/11/16]     Ziyara: [1241]

Tura tambaya