mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Shin akwai saki cikin auren da aka kulla shi ba tare da sigar shari’a ko auren hukuma ba?


Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
Assalamu alaikum warahmatullahi ta’ala
fatan samun amsa cikin gaggawa daga dukkanin muminai zuwa ga samhatus-sayyid ayatollah al’uzma adil-alawi (h) kan wadannan tambayoyi hatta mu fahimce su da shakali bayyananne
Tambaya ta farko :mace da namiji sukai aure aka shirya musu biki sai dai cewa ba’ a kulla igiyar aure ta shari’a hakama daga hukuma, bayan tsawon lokaci sai suka rabu har akai tsawon shekara da rabuwarsu da juna, shin wannan mata idan taso yin auren da’imi ko na mutu’a shin ya zama wajibi ta nemi saki da kuma yin idda ko kuma za tai wani auren ne ba tare da saki da idda ba, muna fatan samun gamsashshiyar amsa kan wannan tambaya ?
Tambaya ta biyu: mace da namiji sai sukai auren hukuma kadai ba a kulla musu sigar shari’a ba bayan wani lokaci sai sukai saki sakin hukuma kadai banda na shari’a suka rabu da juna, a takaice dai babu auren shari’a babu sakin shari’a, to idan wannan mata taso yin wani aure sabo da wani mutumin daban auren mutu’a ko na da’imi shin wajibi sai ta nemi saki na shari’a da kuma yin idda ta shari’a alhalin batai auren shari’a ba ma’ana dai babu igiyar aure da wancan mutumin da suka zauna a baya tsakaninsu hatta ma ai batun kwance igiyar. Muna fatan samun gamsashshiyar amsa ?
Tsokaci : wannan tambayoyi guda suna daga cikin batutuwan da aka jarrabtu da su tare da ban takaici mai tsanani
shaik jawed bako

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Saki ya hannun wanda yake da iko da shi hakan na tabbatuwa bayan kulla igiyar aure a shari’ance lallai shi saki na kaucewa tare da kaucewar maudu’insa, saboda haka babu maganar saki, amma idan sun kasance sun jahilci hukunci ko maudu’i  suna daga mukassirai to saduwarsu da juna zata kasance shubuha dole ne su rabu da juna tare da sabi halin, sannan ita idda shari’a tana doruwa ne kan saki tunda shi sakin bai kasance sakamakon rashin igiyar aure  daga babin rashin samuwar maudu’i, wajibi kansu shi da ita su tuba su nemi gafarar ubangiji

2-idan auren hukuma ya zama ya tattaro sharudda da ma’anar zartar da sigar aure daga wurga igiya da karba lallai zai zama ya zartu a sharia’ance haka lamarin yake dangane da sakin hukuma da shima zai kasance ya tattaro dukkanin sharuddan saki kamar yadda aka ambace shi cikin litattafan fikihu ya ginu kan hakan da za ta nemi yin aure da wani mutumin daban ya zama wajibi ta nemi sakin hukuma ko na shari’a  hakama dole ne tayi idda, na’am da ace auren hukumar zai kasance tsuran yarjejeniya tsakanin mace da namiji to mas’alar zata zama irin ta farko da amsarta. Allah ne mafi sani
Tarihi: [2017/11/16]     Ziyara: [862]

Tura tambaya