mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Me ake nufi da Sidkul Urfi wanda muke yawan ganinsa cikin Risalolin taklidi, shin ma’auni shine urfin gamagarin mutane ko kuma na Fakihai?

1-Shin urfi daya guda daya ne ko kuma yanada da yawa?
Idan ya kasance guda daya ne to me ya sanya ake samun sabani cikin iyakance maudu’i zaka samu fakihi yana cewa kaza dalilina kaza
2- me ake nufi da wujdan menene ma’auninsa? Shin guda daya ne ko kuma yana sabawa daga wannan mutumin zuwa waccan

1-Shin urfi daya guda daya ne ko kuma yanada da yawa?

Idan ya kasance guda daya ne to me ya sanya ake samun sabani cikin iyakance maudu’i zaka samu fakihi yana cewa kaza dalilina kaza

2- me ake nufi da wujdan menene ma’auninsa? Shin guda daya ne ko kuma yana sabawa daga wannan mutumin zuwa waccan

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Manyan malamai sun samu sabani cikin zayyane urfi da bayanin maudu’ancinsa, daga cikinsu akwai wadanda suke ganin cewa fakihi ne da kansa ke zayyane da ayyana urfi, sai dai cewa yana nesantuwa da fakihancinsa yayin ayyana maudu’i, bawai gama garin mutane misalin malam mai sayar da turare da malam mai kayan miya ba, lallai da ace gama garin mutane ke zayyane shi to da hakan ya lazimta komarda malami zuwa wurin jahili, wannan shine ra’ayin da malaminmu Ustaz Ayatollah Shaik Jawad Mirza Tabrizi cikin darasinsa na bahasul karijul fikhu. Sai dai cewa malaminmu Sayyidul Ustaz Ayatollah Mar’ashi Najafi shi ya tafi kan cewa urfi sune malam mai sayar da kayan miya da malam mai turareda misalsalansu, shi urfi yana kofar gidanka, kuma hakan bai lazimta komar da malami zuwa ga jahili , sakamakon saninsa ga maudu’in a wannan lokaci shi fakihi yana matsayin wanda ya jahilci maudu’in sai ya koma garesu, kamar yanda Muhakkik mai girma Kashiful Gidayake fadi: lallai shi fa fakihi duk inda yakai ga ilimi da sani to fa bai kubuta ba daga bukatuwa daga gama garin mutane cikin zayyane maudu’an hukunce-hukunce daga maudu’an da urfi ke zayyane su koma bayan shari’, amma mu ra’ayin shine warware mas’alar filla-filla tareda la’akari da muhallan da ake da sabanin maudu’ai, wani lokacin zayyanewar na hannun fakihi wani lokacin kuma na hannun  ba’ame gama garin mutum.

Allah ne masani

Tarihi: [2019/4/16]     Ziyara: [884]

Tura tambaya