mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

kissar hijabi

Salamu Alaikum

Ina son bayyanawa Sayyid kissata sakamakon na rasa nutsuwa kan abinda yake dam, da farko dai ni musulma ce sai dai cewa tareda haka mahaifana suna da banbancin mazhaba, mahaifiyata musulma ce `yar shi’a shi kuma mahaifina daga sunna, sai dai cewa cikin godiyar Allah na taso cikin mahalli mai zaman lafiya mara ta’asubbanci, ina yin sallah kamar yanda babata take yi ina kwaikwayonta cikin komai tareda kiyaye girma mahaifina da neman yardarsa saboda yardar Allah na karkashin yardar iyaye.

 

Salamu Alaikum

Ina son bayyanawa Sayyid kissata sakamakon na rasa nutsuwa kan abinda yake dam, da farko dai ni musulma ce sai dai cewa tareda haka mahaifana suna da banbancin mazhaba, mahaifiyata musulma ce `yar shi’a shi kuma mahaifina daga sunna, sai dai cewa cikin godiyar Allah na taso cikin mahalli mai zaman lafiya mara ta’asubbanci, ina yin sallah kamar yanda babata take yi ina kwaikwayonta cikin komai tareda kiyaye girma mahaifina da neman yardarsa saboda yardar Allah na karkashin yardar iyaye.

Lokacin da na cika shekaru 15 na yanke shawara sanya hijabi amma sai mahaifina yaki laminta da wannan shawara domin ya kasance cikin damuwa kan kalubalen da zna fuskanta daga sauran yan mata irina da cewa kuma lokacin da zan shiga jami’a zanyi watsi da shi, na dau shekaru bana sanya hijabi har lokacin da na kamala jami’a na samu aikin koyarwa a daya daga makarantun kiristoci. Lokacin da na shagaltu da aiki na fara karbar albashi sai na fara jin cewa inada yancin tunani da zabar abinda nake so a wannan lokaci sai na kara yanke shawara da zan sanya hijabi, na ci shekaru biyu da fara aikin koyarwa sai na je wajen babana na bayyana masa shawarar da na kara yankewa kan sanya hijabi sai dai cewa a wannan karon ya goyi bayana kan haka sai dai cewa ban san da cewa duk wata malama idan zata bar aiki dole ta sanar da shugabanta kafin biyar ga watan tammuz, na yi bakinciki matuka hakan ya tilasta yin hakuri da cigaba da aikin, a yanzu Alhamdulillah ina dab da kammala wannan aiki, sai dai cewa ina cikin damuwa da tsoron ban sani ba shin inada uzuri wurin ubangiji ko kuma na aikata sabo?

Shin wajibi kaina in sanya hijabi sai in cire lokacin da na shiga makaranta sakamakon ba zasu laminta da sanya hijabi ba.

Hakika in neman gafarar Allah kan wannan zunubi, kuma in bakin kokarina kan ganin na sanya hijabi na samu kwanciyar hankali a tsahon wannan lokaci ina sanya kaya masu lullube jiki don gudun kada in sabawa Allah.

Sai dai cewa abin ban takaicin banda damar sanya hijabi har sai kammala wannan lokaci, ni dai ina da yakinin cewa Allah ya san halin da na samu kaina zai tausaya mini ne ko kuma zai kama ni da laifin aikata sabo?

Na manta gaya maka cewa ina taklidi da Sayyid Kamna’i (h)

Daga karshe ina godiya da bani lokaci da taimakonka.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai   

Tabbas hijabi umarni ne daga umarnin Allah kuma wajibi ne daga wajibai kamar sallah da azumi, dian wani al’amarin duniya ya hana lamarin ubangiji to lallai ana fifita lamarin ubangiji kan lamarin duniya. Lallai hakan yana daga jarrabawa kan takawa da tsentseni, idan kika gabatar da hakkin Allah kan hakkin mutane da hakkinki cikin mahallin rayuwarki lallai Allah zai daukaka sha’aninki zai bude miki kofofin rahamarsa da arzikinsa na halaliya, shi kowanne sabo dai sabo ne karshensa kuma wuta ita kuma ta kewaya da masu aikata sabo da kafirai sai dai cewa mutane sun gafala daga hakan, a barzahu ranar a da za a yaye rufi daga idanuwa da basira kowa da kowa zai idonsa zai bude tangararau  zai ga komai tar zai ga cewa shi yana tsakiyar wuta zai ga cewa shi yana ni’imtuwa kamar yanda dabbobi suke ni’imta ko kuma mafi bata daga garesu, kin sanya hijabi ga mace sabo ne sai dai idan ya kasance cikin halin tilas da rashin zabi ta yanda aka dora makami kanta da barazanar kasheta a iya wannan lokaci tanada uzuri, amma da wannan barazana ta kauce dole ta cigaba da sanyawa.

Allah ne mai taimako
Tarihi: [2019/3/3]     Ziyara: [609]

Tura tambaya