mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

SU WANENE WADANDA KALMAR YABO TA GABATA A KANSU

Salamu Alaikum
Ya zo cikin littafin Nahjul Balaga daga zantukan Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata gareshi:
: فلو إن الباطل خلص لم يخف على ذي حجى . ولو إن الحق خلص لم يكن إختلاف، ولكن يؤخذ من هذا ضغث ومن هذا ضغث فيمزجان فيجيئان معا فهنالك إستحوذ الشيطان على أوليائه، ونجى الذين سبقت لهم من الله الحسنى
Da ace karya ta fito ta bayyana da ba a ji tsoranta ba kan dukkanin ma’abocin hankali, da ace gaskiya ta tace da sabani bai kasance ba, sai dai cewa an kwaso daga can da can an cudanya su tare da junato fa anan ne shaidan yake ribata kan waliyyan Allah, sai wadanda Kalmar yabo daga Allah ta gabata garesu su samu tsira daga wannan tarko.

Tambaya tana kan Kalmar karshe da ta zo cikin zancan Sarkin Muminai wato (sai wadanda Kalmar yabo daga Allah ta gabata a kansu su samu tsira) su wanene wadanda Kalmar yabo ta gabata a kansu? Wanne abu suka tsinka da har suka kai ga samun shiga cikin kulawar ubangiji da kiyayewarsa matsarkaki.
Ina godiya da ludufinku.

da sunan Allah mai rahama mai jin kai

su ne Annabawa da Wasiyyai da Waliyyai sannan Muminai maza da mata haka dai da ire-irensu, kadai dai Allah yana tseratar da wanda ya kasance mumini (muna tseratar da muminai) kamar yanda ya zo a cikin kissar Annabi Yunusa da istigfarinsa da yayi a cikin Kifi.

Kadai dai su basu gurbata halittarsu da aikata zunubai sakamakon kiyaye tsarin halittarsu ta kan shiriya da tauhidinsu suka azurta da kasance cikin da’irar kulawar ubangiji ya Allah ka sanya mu a cikinsu Amin.

Tarihi: [2019/9/26]     Ziyara: [489]

Tura tambaya