mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

yazo cikin hadisin Annabi (s.a.w) yace:

yazo cikin hadisin Annabi (s.a.w) yace:

قال رسول الله ‘: من لم يعرف امام زمانه مات ميتة الجاهلية ميتة كفر وضلال ونفاق.

Duk wanda bai san Imamin zamaninsa ba ya mutu mutuwar jahiliya mutuwar kafirci da `bata da munafunci.

yazo cikin hadisin Annabi (s.a.w) yace:

قال رسول الله ‘: من لم يعرف امام زمانه مات ميتة الجاهلية ميتة كفر وضلال ونفاق.

Duk wanda bai san Imamin zamaninsa ba ya mutu mutuwar jahiliya mutuwar kafirci da `bata da munafunci.

Hakika wanda bai san Imamin zamaninsa da sani na Akida da Imani cikin zuciya kamar sanin Allah da Manzonsa, ya zama ya yi Imani da shi da Imamanci da Halifanci da wasiyyar Manzon Allah (s.a.w) lallai shi Imamanci cigaban Annabta ne cikin kareta da kiyayeta  daga tozarta da kuma yada sako da tsayar da shi tsakankanin  mutane da `dabbakawa cikinsu, kamar ammabta ta kasance mikewa da cigaban tauhidi, duk wanda bai san Imamin zamaninsa ba da wannan sani kuma bai samu alaka da shi ba da igiyar wilaya da Imamanci da `da’a to lallai shi bai yi aiki da wasiyyar Annabawa da Manzanni ba, ballantana aiki da wasiccin Allah cikin Talikai, babu shakka duk wanda ya kasance cikin wannan yanayi tabbas mutuwarsa zata kasance mutuwar jahiliya, ma'ana mutuwarsa zata ginu kan harshashin jahilci koma bayan ilimi da hankali.

Sakamakon kasantuwar mutuwa matsayin tacewar rayuwa da karshenta to duk wanda mutuwarsa ta kasance Jahiliya babu shakka da kokwanto rayuwarsa baka dayansa ta kasance kan Jahiliya, kamar yanda ya zo cikin Hadisi daga Annabi (s.a.w)    

 (كما تعيشون تموتون، وكما تموتون تعيشون (عوالي اللألئي 4:72).

Kamar yanda kuka ratyu haka zaku mutu kamar yanda kuka mutu haka zaku rayu.

Idan rayuwarsa ta kasance rayuwa ta jahilci to tabbas abinda ke lazimtarta dukkanin bangarorinta da sassanta zasu kasance cikin da’irar jahilci.

Babu shakka cewa jahilci yana daga duhu kamar yanda ya zo cikin hadisin rundunar jahilci da rundunar hankali, saboda haka a wannan lokaci rayuwarsa zata kasance rayuwar duhu babu haske cikinta, sai ka sameshi yana fagarniya da dimauta cikin jahilci babu haske gareshi babu mai shiriya gareshi har zuwa marhala ta karshe a rayuwarsa, a dabi’ance zai zamana ya kare rayuwarsa cikin jahilci ya kuma mutu Jahili, kan wannan asasi bai zai taba yiwuwa rayuwarsa ta kasance rayuwa ta hankali cikin tamabrin haske da bayyanuwa cikin tasarrufat dinsa da motsinsa da sukuninsa da gabatarsa da ja bayansa ba, lallai shi hankali an halicce ne daga haske.

Shi hankali shine wannan abu da aka bautawa Allah da shi aka kuma samu Aljanna da shi, ba zai yiwu wanda ya gina rayuwarsa kan jahilci ba ace kuma rayuwarsa da mutuwarsa su karkare da hankali da haske, tareda haka lahirarsa ita ma tra zama haske (idan mutum ya mutu kiyamarsa ta tsayu) idan ya kasance Mumini haske zai dinga zazzagawa gabansa da bayansa ya kuma rike hannunsa zuwa cikin Al’arshi cikin matsugunar gaskiya wurin Sarki Mai iko cikin inuwar Al’asrhin Allah matsarkaki.

Ita rayuwar lahira itace madawwamiyar rayuwa wacce take kasance sakamakon mutuwa ita kuma mutuwa natijar rayuwa ce, sabida haka ma’auni da yake banbance rayuwar hankali da rayuwar jahilci shine mutuwa, lallai ita mutuwa itace halka da igiyar sadarwa tsakankanin rayuwa biyu wato rayuwar duniya da rayuwar lahira.

Sannan duk wanda bai san Imamin zamaninsa ba hakikanin sanin a zamanin Gaiba Kubra (fakuwa) lallai ba zai taba kasance mai jiran bayyanarsa da tsayuwarsa da gyaransa domin cika Kasa da adalci da daidaito bayan cikarta da zalunci da danniya, sannan daga cikin alamomin rayuwar jahilci shine mutum ya kasance baya tsimayi da kuma jiran Mai kawo gyara na hakika a doran kasa don cikata da adalci, ita rayuwar ilimi tana cika da tabbatuwa ne da sanin Imamul Zaman (Af)

Tambihi mai muhimmanci gaske:

Tana yiwuwa a zahiri Mumini ya kasance cikin zahirin rayuwarsa yana rayuwa cikin hallarar Imani kasanctuwar yana kiyaye sallah da azumi da kuma yawaita karanta Kur’ani Mai girma ka same shi yana zaman ittikafi cikin masallacin Annabi Mai daraja, cikin Mihrabin Annabi (s.a.w) yana sallah yana bada huduba kan Mimbarinsa sai dai cewa tareda haka sai ka sami rayuwarsa rayuwa ce ta Jahiliya cikin inuwar kafirci da munafunci lallai inuwar kafirci da munafunci baki dayanta jahilci, zahirin rayuwarsa cikin ibada cikin mabayyanan Imani, sai dai cewa tareda haka rayuwarsa rayuwa ce ta Jahiliya sakamakon rashin sanin Imami zamaninsa kamar yanda shugabar matayen duniya tayi ishara zuwa ga haka cikin hudubar da ta yi wacce aka fi sani da huduba Fadakiya ku duba Biharul-Anwar j 29 sh 220 cikin kafa hujjarta kan mutanen sa suka yi mata kwacen halifanci suka nesantar da Imami jagoran gaskiya daga mukaminsa hakkinsa suka zauna a mahallin da bana su ba bisa zalunci da danniya da kwace da gasabi, sai ta kafa musu hujja da fadin Allah ta’ala:        

﴿ أَفَحُكْمَ الْجَاهِلِيَّةِ يَبْغُونَ وَمَنْ أَحْسَنُ مِنْ اللَّهِ حُكْماً لِقَوْمٍ يُوقِنُونَ ﴾ (المائدة: 50).

Yanzu hukuncin Jahiliya suke nema wane ne yafi Allah kyautata hukunci ga mutane sa suke yakini.

Saboda haka duk wanda bai san Imamin zamaninsa ba bai kuma jira bayyanarsa cikin Gaiba Kubra rayuwarsa ta kasance rayuwa ta Jahiliya da duhu, karshen rayuwarsa zai zamana mutuwar Jahiliya.

Tarihi: [2020/4/22]     Ziyara: [1226]

Tura tambaya