mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

MENE NE HUKUNCIN WANDA YA BOYE ILIMI

Ya zo cikin haidisi mai daraja cewa hikima shine ilimi da ma’arifa idan ka yi rowar ta ga ahalinta to hakika ka zalunci ma’abota hikima, shi kuma zalunci abu ne da yake da muni a hankalce da shari’ance, haka idna ka badata ga wanda ba ahalinta ba to hakika ka zalunci hikima, ta yiwu malami ya boye ilimi daga barin wadanda ba ahalinsa

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ya zo cikin haidisi mai daraja cewa hikima shine ilimi da ma’arifa idan ka yi rowar ta ga ahalinta to hakika ka zalunci ma’abota hikima, shi kuma zalunci abu ne da yake da muni a hankalce da shari’ance, haka idna ka badata ga wanda ba ahalinta ba to hakika ka zalunci hikima, ta yiwu malami ya boye ilimi daga barin wadanda ba ahalinsa domin yin hakan ya zama tilas saboda rashin yin hakan zai kasance zalunci kan ilimi, amma boye shi daga ahalinsa lallai hakan abin kyama ne, lallai yand aal’amarin yake kamar yanda Allah ya wajabtawa mai koyo zuwa koyo haka ya wajabtawa mai koyarwa da ya koyar ilimi, ya zama dole a yada ilimi lallai zakka ilimi shine yada shi ga ahalinsa idan ko ba haka kamar anyi shuka ne a bushashshiyar kasa kamar yanda wasu suke ajiye ilimi da ma’arifa cikin kasar da ta cike da zunubi da sabo lallai hakan zai zama wulakantar da irin shuka, kuma yana ishara kan cewa mai shukar bai da hankali  da hikima da adalci, domin hikima da hankali da adalci shine ajiye abu a muhallinsa, sannan kan fadada wannan mas’ala ta boye ilimi muna cewa wani lokaci dole a boye ilimi wani lokacin kuma dole a fito da shi, tana iya yiwu a mahangar Fikhu ya zama haramun.

Allah ya bar cikin alheri. 
Tarihi: [2019/10/13]     Ziyara: [523]

Tura tambaya