mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

NA AIKATA WANI LAIFI DA NAKE JIN TUBANA DA ISTIGFARINA BA ZASU KARBU BA

Salamu Alaikum wa rahamatullahi

Fatana na ga Samahatus Assayid kuma ina muku fatan dawwama cikin lafiya da alheri.

Dan’uwana mai girma ina neman afuwa bisa takura muku da nayi ina rokon ku aika da wasikata kai tsaye zuwa Samahatus Assayid matukar da kuna da damar aikata hakan sannan kuma ku aiko mini da amsar da ya bayar zan kasance mai muku godiya.

Salamu Alaikum wa rahamatullahi

Fatana na ga Samahatus Assayid kuma ina muku fatan dawwama cikin lafiya da alheri.

Dan’uwana mai girma ina neman afuwa bisa takura muku da nayi ina rokon ku aika da wasikata kai tsaye zuwa Samahatus Assayid matukar da kuna da damar aikata hakan sannan kuma ku aiko mini da amsar da ya bayar zan kasance mai muku godiya.

Ina rokon dan’uwa da ya sadar da wasikata sakamakon sabon da na aikatawa kaina ni ban ma sani ba shin na cancanci gafara nayi istigfari da yawa na kuma nemi tuba ban sanik ko dai kawar motsa fatar bakina kadai nake, duk sanda na dauki alkawarin dai na aikata laifi sai in tsinci kaina cikinsa.

Ina bukatar tsarkakuwa daga datti da kazanta sai dai cewa duk wani tattaki da na taka sai in samu kaina cikin jahilci kuma raina ta kasance mai yawan umarni da mummuna, ina fatan rahamar Allah da kuma sa ran ya dubi baki dayan lamarina.

dan’uwa mai daraja ina sarai ina kuma fatan wasikata ta isa zuwa hannun Samahatus Assayid cikin gaggawa kafin Iblis ya cudanya kazaman hannayensa cikin kwakwalwata da zuciyata kafin fushin Allah ya sauka a kaina, gabanin batana cikin wannan kwazazzabo in wanzu daurarriya biyewa son raina ya zamanto na cancanci wanzuwa cikin jahannama, ina fata ina kuma sarai in kamsasa da gafarar Allah da kuma neman gafara ta gaskiya wacce na jima ina fatan samunta, na jima ina mafarkin samun wannan albarkacin Fatima (a.s) kamar yanda nake mafarkin ubangijin yayi mini rahama

 

«وكَمْ من ثَناء جَميل لَستُ اَهلاً لَهُ نَشَرتَهُ»،

Nawa daga yabo da ban cancance shi amma kuma sai ka yada shi.

 

Sai dai cewa na munana suna cikin al’umma da nake rayuwa cikinsu da abinda na gogayya da shi daga yanayi da na sha azaba cikinsa, yanzu_ tir da taguwar da son raina ya hau na kuma biye masa, kaiconta daga abinda ta zace-zacenta ta sawwala mata da kuma burace-buracen son rai, tir da ita da tsagerancinta ga shugabanta majibancin lamarinta.

Ya shugabana ni yanzu hannu na babu komai cikinsa da yayi tanadi daga aiki ya ma munana, da kuma harshe da ya kurmantu sakamakon aikata zunubi, da makauniyar basira da ganinta ya makantar da ita da zuciya da ta yi bakir kirin, ni da kaina duk mun halaka, ya shugaba ya mai girma jikan Fatima Zahara (a.s) ni na san ni ban cancanci zama wanda ma zata kawo muku kukanta ba ko kuma neman wata bukata sai dia cewa ina fatan kuyi mini wata addu’a da zata tsarkakeni ina daga halakar da nake ciki wacce na jefa kaina ciki, ina rokonka da ka kebanceni da wata addu’a daga gareka musammam cikin wadannan kwanaki na juyayin Imamul Hujja Allah ya gaggauta bayyanarsa bisa shahadar kakanku Imamul Husaini (a.s) wanda yak e karbar ta’aziyya daga gareku safe da yamma da idanuwansa masu zubar da hawayen jini, ku mini sadaka da digon addu’a albarkacin addu’arku ina kasance farin ruwa mai dadi kan zuciyar Abu Abdullah (a.s) sanyin idon kakarku Assidika Ashshahida, ni na san ban cancanci kallo ko da kwaya daya ba sai dai cewa na yarda in kwankwasa kofarku lallai ku tsarkaka ne albarkacinku in kasance taimako ga Ahlin Isma shi ya fi alheri daga in kasance mai fagarniya da rudewa ko kuma kasance yar tsana a hannun Shaidan in zama mai biyewa wannan duniya wulakantacciya.

أي ربّ جللني بسترك بستر عمتكم زينب(سلام الله عليها)

 

Ya ubangiji ka lullubeni da labulenka da labulen gwaggpn Sharifai Zainab (a.s).

 

Dan’uwana mai daraja ka rokar mini Assayid ya kebanceni da addu’a domin samun dacewa da gafara da biyan bukata da suttura da afuawa da lafiya da kyakkyawan karshe.

Allah ya kare Assayid ya kuma kareku ina mika godiyata gareku.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ya Abu Salihu Almahadi ka riskemu, Allah shine aminci daga gareshi aminci yake gareshi aminci yake komawa, amincin Allah ya tabbata a gareku yaku masoyana masu daraja yan’uwana maza da mata gabas da yamma, amincin Allah gareki `yata mai daraja mumina mai Imani da Fatima `yar gidan Imani Allah ya dawwamar da imaninta Allah ya tasheki da Imaninki duniya da lahira tareda shugabarmu shugabar matan duniya Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta.

Wasikarki da kamshin Imani da wilaya ke tashi daga cikinta ta zo hannuna na kuma yi godiya ga Allah kasance kin aiko da wannan wasika zuwa gareni wacce alkaminki ya kwararar da falala da kyawawan bayanai, ina rokon Allah Azza wa Jalla da ya dawwamar da wannan ni’ima gareki ya kuma yi kari cikin taufikinki da faranta miki duniya da lahira.

`yata mai daraja wannan ikirari da zunubi ya fi kyawunta ki kebance kiyi shi daga ke sai ubangijin talikai bawai tareda bayinsa dare da rana cikin kowanne lokaci daga wasiwasin Iblis da rundunarsa daga mutane da Aljanu, sannan fadinki (kafin Iblis ya cudanya kazaman hannuwansa cikin kwakwalwata da zuciya) samsam wannan Magana bata dace tama iya yiwuwa wannan fadin naki ya kasance daga gareshi alhalin ke baki sani ba  kamar yanda fadinki (gabanin fushin Allah ya sauka a kaina) shima bai dace, lallai misalin wadannan kalamai sun fi kyawunta da dadada tsakaninki ke da Allah matarkaki ta’ala, sannan me yasa kike debe tsammani haka, san maganganun naki basu dace ba ki daina siffanta kankanki da cewa surarki ta munana cikin mutane alhalin kina mumina kamammiya mai sanya hijabi mata suna koyi da aikinki suna shiriya da zantukanki da nusantarwarki, matukar dai kin san hanya da kike bi bata da kyawu to ai kln san maganin ciwon da kike fama da shi, sabida haka me ya kawo irin wannan debe tsammani ?! (hakika tsoro da fata haske ne guda biyu cikin zuciyar mumini idan aka auna daya kan daya babu wanda zai rinjaye) bari dai abinda yake bayyana daga ayoyi da riwayoyi shine cewa bawa ya koma ga ubangijinsa yasa rai da rahamarsa fiye da tsoran damkarsa da fushinsa da azabarsa (ya wanda rahamarsa ta gabaji fushinsa) ina ma dai fadin ki (shugabana hannuna babu komai) kin yi wannan Magana zuwa ga hannunki ba hakika wanda shine Allah matsarkak, yayinda nake baki amsar wasikarki a daren juma’a a karfe takwas da rabi ian kan hanyata zuwa gabatar da lacca da zan yi a karfe tara da kwata  sabida haka zan hattama da yi miki addu’a daren juma’a  domin cika ga hannunki da da hannuna albarkacin hannuna zuwa ga hannun Allah shimfidadde mai yawan kyauta da failoli da rahama da jin kai

 (يا دائم الفضل على البرية يا باسط اليدين بالعطية يا صاحب المواهب السنية صل على محمد وآلِ خير الورى سجية واغفر لنا يا ذا العُلى في هذه العشية)

 

Ya mai yawan falala ga mutane ya mai shimfida hannu da kyauta ya ma’abocin kyaututtuka madaukaka kayi salati da Muhammad da iyalansa mafifita kai mana gafara a wanann dare ya ma’abocin daukaka.

 

Maganarmu ta karshe dukkanin godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai.

Tarihi: [2020/3/17]     Ziyara: [1022]

Tura tambaya