b Wanda suka gama makaranta amma basu samu aiki ba da kuma abin da yafi dacewa suyi
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wanda suka gama makaranta amma basu samu aiki ba da kuma abin da yafi dacewa suyi

Assalamu alaikum
Ni saurayi ne dan shekara ishirin da… Alhamdu lillah na kamala karatuna nag aba da sakandare amma sai na samu matsala tsakanin aikina da kuma rayuwa ta na rasa wanne ne yafi dacewa na zaba, akwai cibiyoyin aiki da suka nemeni amma na kasa tsai da magana daya har ya jawo na kai shekara uku da gama karatuna amma ba maganar aiki, ko akwai wata hanya wacce zata taimaka min wurin samun daman zabi?

Da sunan Allah me rahama me jin kai

(وَمَن يَتَّقِ اللَّهَ يَجْعَل لَّهُ مَخْرَجًا وَيَرْزُقْهُ مِنْ حَيْثُ لَا يَحْتَسِبُ وَمَن يَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ فَهُوَ حَسْبُهُ)

Idan ka sanya Allah a alamuran ka kuma kayi tawakkuli da shi sannan ka kasance baka saba masa kuma kana tsaida wajiban ka, Allah zai taimaka maka kuma zai bude maka hanyoyin arziki ta yadda baka tsammani wanda zaka samu kwanciyar hankali da farin ciki da kuma jindadi na rayuwa.

Tarihi: [2016/9/5]     Ziyara: [1064]

Tura tambaya