mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Mene ne hikima da falsafar samuwar Imami?

Me ya sanya Allah Azza wa Jalla ya halicci mutane?
2-bukatuwarmu zuwa ga Jagorori daga Allah?
3-mece ce Falsafa da hikimar samuwar Imami?
4-mece ce falsafar samuwar me kawo gyara a duniya da fakuwarsa?

Me ya sanya Allah Azza wa Jalla ya halicci mutane?

2-bukatuwarmu zuwa ga Jagorori daga Allah?

3-mece ce Falsafa da hikimar samuwar Imami?

4-mece ce falsafar samuwar me kawo gyara a duniya da fakuwarsa?

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai

Hakika Allah shi ne tsantsar kamala daga kamalar tsantsar kamala kamalarsa ta kwarara, kamar yanda daga kamalar rana kwarara tarsashin haskenta yake, sai ya halicci halittu daga kamalar kamala, kamar yanda ya zo cikin hadisi Kudusi daga Allah matsarkaki

كنت كنزاً مخفياً فأحببت أن اُعرف فخلقت الخلق لكي أعرف

Na kasance boyayyar taska sai na kaunaci a sanni sai na halicci halitta domin sanina.

Sanin kamala a larurance yana hukunta abinda yake shiryarwa zuwa ga kamala, halittar ayoyi ufuki sasanni da na kankin kai sun shiryar kan samuwar Kamala tsantsa Masanin koma da komai Mai iko kan kowmai rayayye tsayayye Daya tak rak  babu wani abu misalinsa, sannan halitta sun kasance mabanbantan juna bisa la’akari da illoli da ma’alulai kan ka’aidar (Ashraf) hakika mafi daukakar daraja mai dataja na fita daga gareshi mafi kusa-kusa da kusanci gareshi wannan yana lazimta saukowar silsila cikin Kausul nuzuli  har ya kai ga wanda yake kasa da shi, sannan mafi daukakar darajar halittun Allah shi ne Muhammad da iyalansa tsarkaka wadanda Arifai suke kiransu da sunan Hakika muhammadiya, lallai shi ne wanda ya fara gangarowa daga Allah matsarkaki

 (أول ما خلق الله نوري)

Farkon abinda Allah ya fara halitta shi ne haskena.

Shi ne hankali na farko sannan sauran hankula suna dinga sauka sannu-sannu da martabobin samuwa daga Mafi daukaka zuwa Madaukaki har zuwa kan na kasa ya zuwa mafi kaskanta, tamatanshi itace duniya  wacce muke cikinta, sai  Allah ya halicci mutum domin ya kasance mabayyanar sunana mafi daukaka da girma da kuma kyawawan sunayensa da madaukakan siffofinsa, mutum shi ne mafi daukakar halittun Allah, sai Allah ya bijiro da amanarsa zuwa ga halittunsa wacce ta kasance takalifi ne daga wajibi da haramun da sauransu, sai Sama da Kasa suka ki yarda su dauki wannan alkawari amma sai shi mutum ya dauki wannan alkawari , sai ya wayi gari ya zama masaukar wazifofi addini da taklifin shari’a da wannan ne ya daukaka akn sauran halittu saboda shi yana dauke da hankali wanda cikinsa yayi tarayya da Mala’iku ya na kuma dauke da sha’awa, idan ya zamana hankalinsa yayi galaba kan sha’awa sai ya kasance mafi falala da daraja daga Mala’iku  barima zasu zama hadimansa, idna kuma sha’awa tatyi galaba kan hankali zai zama misalin Dabbobi barima ya fi su bata.

Allah shi yake shiryar da mutum ko dia ya kasance mai godiya ko kuma mai butulci, sai ya saukar da litattafai ya aiko da Manzanni domin shiriyar da mutum da samun farin cikinsa ndomi ya kai ga cimma kololuwar kamala wanda shi ne mukamin fana’i da narkewa cikin Allah da wanzuwa tareda shi, wajibi kanka ya kai mutum kayi kokarin kaiwa wannan mukami, shin ka taba yin tunani cikin haka ko kuma kana nan baka gushe ba cikin tunanin me ya sa Allah ya halicci mutum.

2-daga jawabin farko a jumlace  jawabi na biyu ya bayyanu, hakika mutum ya rakkabu ya tattaru daga hankali da sha’awa da Nafsul Ammaratu bis su’I wacce take fizgarsa ya zuwa ayyukan sabo da biyewa sha’awa ta haramun da zunubai da karkacewa gaskiya da bin bata da tsiyata, hakika Allah ya kasance Mai ludufi Mai shiryarwa da nusantarwa kuma yana son bayinsa yana nufinsu da alheri da farin ciki sai ya aiko musu da Jagorori daga gareshi domin shiryar da mutane da kuma bayyana musu alheri daga sharri da banbance gaskiya daga karya, da wahayi ne hankali yake samun taimako don samun tsaftatacciyar rayuwa duniya da lahira, kamar yanda ya aiko da Manzanni da Annabawa Jagorori domin cika hujjarsa kan mutum domin kada mutum ya samu uzurin fadin da dai ka aiko mana da Manzo da mun shiriya, domin kada ya azabtar da mutane ba tareda yanke musu uzuri ba, lallai Allah yana da Hujja mai isarwa wacce daga cikinta akwai wadannan Jagorori daga Allah, Manzanni sun kasance daga masu bushara  da gargadi domin mutane su tsaya da adalci da daidaito.

3-hakika ya tabbatu a muhallinsa cewa ba da ban Hujjar Allah ba da Kasa ta bushe ta nutse da mutanen da suke kanta, da wanzujwar tsarin halitta da na shari’a ne da samuwar Hujjar Allah kan halittu a kowanne zamani kasa ta wanzu, sai dai cewa Hujjar Allah a wani lokacin taka kasnancewa ta zahiri a wani lokacin kuma a boye kamar buya da fakuwar rana bayan girgije, lallai rana tana da tasirinta hatta a halin fakuwarta da buyanta har zuwa lokacin da zata haskaka girgijen da ya boyeta ya kauce ya bushe to haka lamarin yake dangane da Mai kawo gyara a fadin duk duniya Hujjar Allah kan halittunsa lallai shima yana tareda tasirinsa da kasancewarsa hujja hatta lokacin fakuwarsa da buyansa, hakika lallai mu muna nan muna tsimayi da jiran huda da haskakar ranarsa da haskensa domin cika kasa da a adalci bayan da cika da zalunci da danniya.

Allah ya sanya muku tareda ku da dukkanin Muminai maza daga cikin masi tsimayi da jira na hakika daga cikin mafi alherin Shi’arsa da mabiyansa masu shahada gabansa.

 

Tarihi: [2020/6/8]     Ziyara: [467]

Tura tambaya