mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

shin akwai wata hanyar magance ciwo ido


Salam Alailkum. Samahatus Sayyid da Allah akwai wata hanya da zamu iya amfani da suaratu hadid don magance ciwon ido ko kuma wani maganin daga A’imma tsarkaka (as). Kamar dai yanda kuka riga kuka sani hakika ba’arin wasu cututtuka da ciwon ido basu da magani kamar misalin cutar farin ido

 

Salam Alailkum. Samahatus Sayyid da Allah akwai wata hanya da zamu iya amfani da suaratu hadid don magance ciwon ido ko kuma wani maganin daga A’imma tsarkaka (as). Kamar dai yanda kuka riga kuka sani hakika ba’arin wasu cututtuka da ciwon ido basu da magani kamar misalin cutar farin ido.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Hakika akwai wasu addu’o’i don magance ciwon ido wanda ko da yaushe nake karanta su lokacin da nake cikin sujjadar shukur (sujjadar nuna godiya) ina sanya danyatsana kan idanu na sannan in ce:  

وأعيذ نور بصري بنور الله الذي لا يُطفئ)

Ina neman tsari da kariyar hasken idanuna da hasken Allah wand aba ya bushewa.

Sannan ina karanta ayatul kursiyu har zuwa

 (هم فيها خالدون)

Su suna madawwama cikinta.

Sannan in ce:

 (اللّهم أحفظ حدقة عيني بحدقتي عيني أمير المؤمنين علي عليه السلام)

Ya Allah ka kare kwayar idanuna da kwayar idanun sarkin muminai (as)

Kamar yanda ina da littafi da aka bugashi kuma za a iya samun a sayit dinmu sunan littafin

(أخلاق الطبيب في الإسلام)

Ahklak din likita a muslunci.

A fasali na karshe na kawo julmar addu’o’i domin samun waraka daga mafi yawan cututtuka gabbai kuna iya duba shi a sayit.


Tarihi: [2018/12/10]     Ziyara: [540]

Tura tambaya