mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Shin ya wajaba ga wanda yake sulukin irfani ya daina cin nama kwata-kwata

Salamu Alaikum maulana shin wajibi ga mai suluki cikin farko-farkon fara sulukinsa ya yanke cin duk wani abu mai rai


Salamu Alaikum maulana shin wajibi ga mai suluki cikin farko-farkon fara sulukinsa ya yanke cin duk wani abu mai rai.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Makaruhi ne barin cin nama har zuwa tsawon kwanaki 40 kuma duk wanda ya aikata hakan to dabi’arsa zata munana bawai ya zama arifi ba, bari dai zai kasance mai mummunan dabi’u sannan domin kawar da munanar dabi’arsa sai a kira salla cikin kunnensa, sannan cikin dukkanin kwanaki uku mustahabbi ne kaci nama kamar yanda shugaban Arifai manzon Allah (s.a.w) da sarkin muminai da Ahlil-baiti da shugabarmu zahara suka kasance suna yi, lallai sun kasance cikin dukkanin kwanaki uku suna cin nama kamar yanda aka ambaci hakan cikin tarihinsu, saboda haka cikin farkon farawa da karshe ya halasta a ci nama domin shi gangar jiki shi ke daukar ruhi sabaoda haka dole a kula da lafiyar jiki.

Allah abin neman taimako.
Tarihi: [2018/12/8]     Ziyara: [576]

Tura tambaya