mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Yadda za ai galaba kan sha`awa jinsi sannan menene mafita daga mutanen da suke yawan ziyartar zaurukan batsa da suke rushe kyawawan dabi`u?

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Mafita kadai itace jin tsoron Allah da kuma tunawa da mutuwa da kwanciyar kabari a kowanne lokaci tareda da lura da zurfafa tunani da kuma tunawa da cewa nan kusa ba dadewa mutum zai riski wanda `yan`uwansa da ke kwance a cikin kabari,

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

 

Mafita kadai itace jin tsoron Allah da kuma tunawa da mutuwa da kwanciyar kabari a kowanne lokaci tareda da lura da zurfafa tunani da kuma tunawa da cewa nan kusa ba dadewa mutum zai riski wanda `yan`uwansa da ke kwance a cikin kabari, sannan ya yawaita son Allah saboda shi soyayyar ubangiji idan ta shiga zuciyar bawa tabbas zai yi watsi da biyewa sha`awe sha`awe da son jin dadi na haramun zai kuma kasance yana jin kunyar ace ya kalli fima fiman batsa domin ya san cewa Allah yana ganinsa  yna jinsa lalle kuma shi yafi kusa da shi daga jijiyar wuyar, da Allah ka kaddara cewa mahaifiyarsa tana zaune tareda shi shin zai iya kallo amsa shine ba zai kalla ba, to yaya kuma idan Allah ne tareda shiwanda shi yana tareda ku a duk inda kuke lalle yafi dacewa ace ya bar wannan aiki na haramun a aikace da ikirari ya yi kuka daga wanda ya aikata a baya ya kuma nemi gafara yaji kunyar Allah ya bar aikata wannan mummuna aiki na haramun sakamkon jahilci da gafala da sharrin shaidani da ya cuna shi ya maida shi jakin iblis da yake kai shi inda ya ga dama, shin yanzu zaka yardarma kanka ka zama jakin iblis `dan lis.

Tarihi: [2017/4/22]     Ziyara: [1178]

Tura tambaya