mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wacce hanya ce zata kai mutum zuwa ga kamala

Salam Alaikum
Wacce hanya mutum zai bi domin kaiwa ga kamala sakamakon sanin cewa halittarsa ta gurbatu cikin wannan duniya, shi yanzu ya dau damara yayi niyya ya dogara da Allah yayi shirin shiga hanyar da zata kai shi zuwa ga Allah, sayyid muna fatan zaka rike hannayenmu kuma muna fatan kaima addu’a ta musammam.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Masana ma’arifa suna cewa farkon masauki daga masaukan masu suluki zuw aga Allah matsarkaki shine (farkawa)

Sannan (tuba) da kuma komawa zuwa ga ubangiji da yin istigfari da tsarkake niyya haka zai ketare marhaloli da masaukaki baki dayansu har sai ya kai ga zuw aga mukamin fana’i da wanzuwa tare da Allah lallai wadancananka shine rabauta mai girma.

Kayi bakin kokarin cikin ganin kayi aiki kana mai tsarkake niyya. Sannan ka nisanci zunubi baki dayanka, kamar yanda sarkin muminai Ali (as) yace:

كما قاله أمير المؤمنين علي× والذي منه أن يذيب لحم المعصية ويثبت مكانه لحم الطاعة وفقك الله لما فيه الخير والسعادة.

Shine wanda naman da ya tofo daga sabon Allah yake narkewa daga jikinsa sannan naman da’ar Allah yam aye gurbinsa .

Allah ya datar da kai abinda cikinsa alheri yake da farin ciki.

Tarihi: [2018/12/15]     Ziyara: [616]

Tura tambaya