mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Takaitaccen tarihin ba’arin Malamai cikin yanda suke kwadayi da rawar jiki cikin yin sallah akan lokacinta

Salamu Alaikum.
Karkashin zamanku da Malamai ku dan bamu takaitaccen tarihi cikin yanda suke kwadayi da rawar jiki cikin sauke sallah a kan lokacinta, da sannu zan ambaci haka cikin abinda na nakalto daga gareku cikin littafi.

Salamu Alaikum.

Karkashin zamanku da Malamai ku dan bamu takaitaccen tarihi cikin yanda suke kwadayi da rawar jiki cikin sauke sallah a kan lokacinta, da sannu zan ambaci haka cikin abinda na nakalto daga gareku cikin littafi.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ina neman uzuri kuma shi uzuri wurin mutane masu karamci karbabbe ne, zan Ambato maka daga malamina Ayatullahi Al’uzma  Assayid Najafi Almar’ashi Allah ya tsarkake sirrinsa, hakika na yi sallah a bayansa kusan shekaru daidai har 25 ban taba samunsa ya Makara a sallarsa tun daga Alfijir har zuwa sallolin dare, ya kasance yana sallatarsu a kan lokaci a cikin jam’i cikin Haramin Assayada Ma’asuma amincin Allah ya tabbata a gareta, kamar yanda ya kasance al’adarsa tsawon shekaru 70, hakika na kawo haka cikin littafin (Kabsat fi Hayatil Assayidina Ustaz) idan kana da sha’awa sai ka duba littafin domin ka samu damar ambatar inda kaga maganar, ina rokon Allah ya datar da kai kada ka manta damu cikin addu’a Allah kuma ya sanya ka daga cikin masu sallah a kn lokaci da sharuddanta da ladubbanta amin  

Tarihi: [2021/4/26]     Ziyara: [457]

Tura tambaya