mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wace hanya ce tafi dacewa wanda zan iya sanya gidana da kuma zurriya ta cikin nutsuwa, mutunci, sadaukarwa ga Allah, zuhudu da kuma takawa?

Assalamu alaikum warahmatullah
Ta wace hanya tafi dacewa da zan iya sanya gidana da kuma zurriya ta cikin nutsuwa, mutunci, sadaukarwa ga Allah, zuhudu, takawa, sanin Allah da manzon sa da kuma iyalan gidan sa wato sani na haqiqa? Kuma Allah ya azurtasu da abotan rayuwan zaman aure na gari, kuma sukasance gidan ilim? Sanann su kasance masu tarbiyya?

Da sunan Allah me rahama me jin kai

Idan mutum na so ya sanya iyalan sa cikin wadannan sifofi da aka Ambato, ya kamata ya karanci hanyoyin da suka fi dacewa don wadannan siffofin ado ne ga gidan mutum, kamar yan da ake cewa duk wanda ya ke yawaita karanta Al’qur’ani a cikin gidan sa da sauti me dadi safe da rana  kuma ya kasance lokacin sallah nayi zai tashi yayi sallah akan lokaci, idan ya kasance ya yawaita yin hakan gidan sa zai kasance cikin haske da kuma annashuwa, haka idan yana yawan amfani da kalamai masu kyau kuma na gari kuma kana yawaita nuna musu halaye na kwarai wanda suka dace, iyalan ka zasu koyi irin wannan halaye naka, ko da bayan mutuwar ne ka zasu ci gaba dayin irin wannan dabi’u na kwarai saboda ya dawo cikin jini da jikin su.

Tarihi: [2016/8/10]     Ziyara: [1055]

Tura tambaya