b Halittu sune ainahin mahalicci
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Halittu sune ainahin mahalicci

Salamu Alaikum. Na tambayi Sayyid Adil-Alawi dangane da nazariyar Imam Komaini ta wahadatul wujud inda Imam yake cewa (hakika halittu sune ainahin mahalicci) karkashin tafsirinsa kan suratu hamdu shafi 160, amma lokacin da na tambayi Sayyid bai bani gamsashshiyar amsa ba, saboda haka yanzu ina fatan gamsashshiyar amsa daga Sayyid. Allah ya saka muku da alheri.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Gamsashshiyar amsa tana bukatar mukaddima tareda karanta ilumummuka da ma’arifofi da halartar hallarar malamai da hidimarsu da makamantan haka, idan ko ba haka ba zai zama misalin ka cewa kankanin yaro baind ayafi komai dadi shine jima’i, lallai babu shakka ba zai fahimci abinda kake son fahimtar da shi ba matukar dai bai kai matakin balaga ba, haka al’amarin yake kan wannan ilimi da kake tambaya kansa, shima ya zama dole ka kai matakin balagar ilimi kansa, ni kuma bansan komai gameda kai ba, saboda haka idan kana da wani malami da ya sanka sosai ya san cewa ka kai matakin nunar tunani kan wannan ilimi don gudun ka da ka fada cikin maganar (wahadatul wujudul zati) wacce take tukewa zuw aga kafirci, to a wannan lokaci sai yayi maka bayanin abinda Imam Komaini (ks) yake nufi, amma rashin amsa tambayarka bay a daga gazawar wand aka tambaya bari dai ya dogara ne da kai da kayi tambayar.

Allah ne abin neman taimako.

Tarihi: [2019/3/18]     Ziyara: [600]

Tura tambaya