mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Yaya Allah ya kallafawa mutane soyayyar iyalan Annabi

Salamu Alaikum
Na farko: Ta kaka Allah ya dora soyayya iyalan gidan Annabi (a.s) kan mutane tareda cewa soyayya bata daga cikin ayyukan da gabbai suke yi da taklifi yake hawa kansu
Da umarni da hani sabida suna da bayyanannun abubuwa sabida haka Allah yace ( ba zaku taba iya adalci tsakankanin mata) ma’ana cikin soyayya?
Na biyu akwai wata shubuha: lallai Annabi da Sarkin Muminai da yayansa Hassan da Husaini amincin Allah ya tabbata a garesu tsawon rayuwarsu basu iya gina al’umma mai soyayya da wilaya a garesu ba sabida hakane ma lokacin waki’ar Karbala babu wanda suke fita tareda Imam Husaini (a.s) sai yan tsiraru, wacce amsa zaku iya bayarwa kan wannan shubuha


Salamu Alaikum

Na farko: Ta kaka Allah ya dora soyayya iyalan gidan Annabi (a.s) kan mutane tareda cewa soyayya bata daga cikin ayyukan da gabbai suke yi da taklifi yake hawa kansu

Da umarni da hani sabida suna da bayyanannun abubuwa sabida haka Allah yace ( ba zaku taba iya adalci tsakankanin mata) ma’ana cikin soyayya?

Na biyu akwai wata shubuha: lallai Annabi da Sarkin Muminai da yayansa Hassan da Husaini amincin Allah ya tabbata a garesu tsawon rayuwarsu basu iya gina al’umma mai soyayya da wilaya a garesu ba sabida hakane ma lokacin waki’ar Karbala babu wanda suke fita tareda Imam Husaini (a.s) sai yan tsiraru, wacce amsa zaku iya bayarwa kan wannan shubuha?

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai

Wannan taklifi ne na halitta kamar misalign tauhidi da Annabta ya daga cikin halittar Allah da ya halicci mutane a kanta kuma ita halittar mutum dayantacciya mai nuna soyayya ga tsantsar kamala wana shine Allah matsarkaki da dukkanin abinda yake sadarwa gareshi itace jijiya soyayya guda uku: son alheri da son kyawu da tsantsar kamala, madubin kyawun Allah shine kamalarsa kuma sune Muhammad da iyalansa sabida haka soyayya garesu tana cikin hallitar mutum  sai dai cewa kamar yanda cikin mutane akwai wanda yake kafircewa Allah ya gurbata halittarsa da ayyukan haramun haka zalika daga cikinsu akwai wanda yake kafircewa Annabi da iyalansa amincin Allah ya tabbata a garesu, soyayyar Allah da Manzonsa da A’imma ma’asumai yana daga soyayya da ke ajiye cikin halitta bawai iri daya take son mata da yake daga garizar sha’awa na dabbantaka da mutumtaka ba kadai zukata suna rataya da ita ne duk da cewa tana komawa zuwa ga halitta tareda la’akari da cewa tana daga masadik din alheri da kyawu da kamala, amma asali cikin wannan halitta ta Allah shine mutumtaka sannan mutum ne yake bakanta zuciya da aikata sabo idan halitta ta cika da ayyukan haramun lallai Shaidani zai mamayeta yayi galaba kansu duk wanda yayi watsi da A’imma amincin Allah ya tabbata a garesu lallai cikinsa ya cika da haramun kamar shugaban shahidan ya fadawa mabiya Abu Sufyan a ranar Ashura lokacin da ya kirasu zuwa ga Allah matsarkaki amma sai suka ki amsa kiransa sai ya bayyana dalilin da ya hanasu yace: (hakika cikkunanku sun cika da haramun sai Shaidan yayi galaba kanku) kuma duk wanda Shaidan ya mamaye shi zai kasance daga masoyansa ya kuma zama misalinsa kuma duk misalin Shaidan yana cikin wuta tareda Shaidan kamar yanda aya da riwayoyi sukayi bayanin haka.

 Sannan shi taklifi wani lokacin yana kasancewa taklifi na fikhu daga halal da haram sai ya zamana ya rataya kan gabbai a wani lokacin kuma taklifi ne na Aklak zai ta’allaka da zuciya da badini kamar misalin kyawawan malaka da halaye lallai Allah ya kallafa mana hakan kamar misalign haramcin hassada sabida itama tana daga abinda yake gabban badini da yake bayyana a gabban zahiri kamar yanda ake cewa: ita zuciya itace Sarauniyar gangar jiki kuma su mutane suna kan addinin Sarakunansu idan zuciya ta gyaru sauran gabbai sai su gyaru,ita soyayya da kauna suna daga taklifin Allah cikin fadinsa madaukaki (ka gaya musu bana tambayarku wani lada sai soyayya ga makusantana) ita kauna itace dai soyayya tareda tsantsar tace `da’a  tareda bayyanar da ita kan gabbai tareda tsanantawa cikinta duk wanda ya so Husaini amincin Allah ya tabbata a gareshi soyayya zata bayyana cikin ziyartar Imam Husaini lallai cikin kashe Husaini akwai zafi da radadi cikin zukatan Muminai da ba zasu taba sanyaya ba har abada soyayyarsa tana bayyana cikin raya bukukuwa zaman makokinsa kamar yanda mutum yake kasancewa an kallafa masa riko da ingantattun akidu da Allah yayi umarni da su yayi hani daga miyagun akidu shin wannan umarni da hani ba komai bane face masadik din taklifi da ma’anar abinda cikinsa akwai nauyi da wahala, shi taklifi bai kyabantu da aikin gabban zahiri ba bari dai yana ta’allaka da zuciya kamar umarni da hani da suke cikin kyawawan dabi’u.

Ka lura sosai.

Allah ne abin neman taimako.  

 

Tarihi: [2020/11/16]     Ziyara: [333]

Tura tambaya