mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

YAYA MUMINA ZATA KARANTA WANNAN JUMLAR


Yaya mumina zata karanta wannan jumla da ta zo cikin Du’a’u Iftitahu (ya Allah ka aura mana matayen aljanna) ta yaya za ace Imam Sadik (a.s) ya kirayi wadanda suka yaki Imam Husaini (a.s) da sunan wadanda suka yi jihadi kansa cikin wannan jumla:

 

Yaya mumina zata karanta wannan jumla da ta zo cikin Du’a’u Iftitahu (ya Allah ka aura mana matayen aljanna) ta yaya za ace Imam Sadik (a.s) ya kirayi wadanda suka yaki Imam Husaini (a.s) da sunan wadanda suka yi jihadi kansa cikin wannan jumla:

 

اللهم العن العصابة التي جاهدت الحسين

Ya Allah ka tsinewa jama’ar da suka yi jihadi a kan Husaini

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Mumina zata karanta ta ne sakamakon abinda ya zo cikin addu’ar sannan Allah yana da iko ya canja hakan gareta zuwa `yara matasa kyawawa idan ta kasance idan bata da aure Kenan, kamar yanda hakan ya zo cikin hadisai cewa wadanda da basu samu damar yin aure a rayuwarsu ta duniya daga maza da mata da sannu zasu yi aure a ranar lahira mata su auri mazan aljanna maza su auri matayen aljanna, za kuma ayi bikin aurensu a aljanna tareda auren Isa dan Maryam (as) domin cewa shima har ya bar duniya bai yi aure ba.

Allah ne masani.

Amma dangane da amfani da Kalmar jihadi cikin ziyarar Ashura lallai amfani da Kalmar ya kasance da isdilahin lugga wacce ta ke dauke da ma’anar sadaukar da karfi da jurewa wahala da tsanani, wadannan da suka halarci filin Karbala domin yakar shugaban shahidai sun sadaukar da dukkanin karfinsu da tanadinsu daga makamai sukayi dukkinin jihadi cikin kashe tsarkaka daga iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w) da Sahabbansu masu daraja.

 

Tarihi: [2019/10/3]     Ziyara: [423]

Tura tambaya