mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Shin wasan motsa jiki yana cin karo da dabi’un Marja’i

Salamu Alaikum. Sayyid raina fansarka akwai wani bidiyo yana yawo a kafar sadarwa ta youtube wanda yake nuna Sayyid Ali Kamna’I yana hawan tsaunukan duwatsu sannan cikin wannan bidiyo an nuna shi yana wasan volleyball kwallon raga shin bakwa ganin haka yana cin karo da kwarjini da girman mukamin maraja’iyya?
Ku mana bayani Allah ya baku lada

 

da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Samahatus Sayyid fakihi ne, tuni lujunar malaman hauza a birnin Qum mai tsarki suka tabbatar da haka a, sai dai cewa maganganunsa dangane da masu yi masa taklidi hujja amma fa ayyukansa da abubuwan da ya zartar ba hujja bane, wannan shine banbancin da yake tsakanin ma’asumi da wanda ba ma’asumi ba, sannan zahirin zance hakan na cin karo da marja’iyyarsa matukar dai ya kasance a bainar jama’a a fili amma idan ya kasance a kebance tareda `ya`yansa masu girma to bai cutar da marja’iyyarsa ko adalcinsa da jagorancinsa, sannan tama iya yiwuwa tsohon bidiyo ne wanda aka dauka tun lokacin samartakarsa bawai lokacin yanzu da yake jagora da marja’i ba, kadai ya nufi harraka samari da sanya musu shauki da basu karfin gwiwa kan yin wasannin motsa jiki don kiyaye lafiya, lallai kamar yanda masu hikima suke cewa: lafiyayyen hankali yana tareda lafiyayyen jiki, tareda dukkanin wannan shine ka dora aikin dan’uwanka kan inganci har sau saba’in ka bashi uzuri.

Allah ne mai taimako.

 

Tarihi: [2018/7/22]     Ziyara: [636]

Tura tambaya