mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

dama ma’anar fadin imam A.s (lallai zan yi kuka kanka kukan jini maimakon hawaye) hakan na nufin buga karafuna a kai

salamu Alaikum

Gaisuwa zuwa ga Samahatu Ayatullahi Assayid Adil-Alawi Allah kare mana shi

Hakika wata damuwa ta mamaye mutanen yankinmu sakamakon abin da wani daga cikin Limaman masallatai yayi lokacin da ya hau kan mimbari ya kama sukan Maraji’ai, inda yake cewa: (wasu daga cikin Maraji’ai sai ya zo ya ce mana ma’ana fadin Imam (a.s) (lallai zanyi maka kukan jini maimakon hawaye) shi ne dukan kai da karfe ma’ana mu bugi kawukanmu da karafuna, wannan wanne irin batan basira ce haka da wauta!

Muna bukatar bayani daga Akaramakallahu kan maganar wannan limami? Mene ne yake wajibi kan Muminai? shin ya halasta a yi sallah a bayan wannan limami bayan jifan Maraji’ai da yayi da wannan miyagun lafuzza?

Tambaya daga wasu adadi daga Muminai da Garin Safawi –yankin Hijaz

                                                                                                

Salamu Alaikum

Gaisuwa zuwa ga Samahatu Ayatullahi Assayid Adil-Alawi Allah kare mana shi

Hakika wata damuwa ta mamaye mutanen yankinmu sakamakon abin da wani daga cikin Limaman masallatai yayi lokacin da ya hau kan mimbari ya kama sukan Maraji’ai, inda yake cewa: (wasu daga cikin Maraji’ai sai ya zo ya ce mana ma’ana fadin Imam (a.s) (lallai zanyi maka kukan jini maimakon hawaye) shi ne dukan kai da karfe ma’ana mu bugi kawukanmu da karafuna, wannan wanne irin batanb basira ce haka da wauta!

Muna bukatar bayani daga Akaramakallahu kan maganar wannan limami? Mene ne yake wajibi kan Muminai? shin ya halasta a yi sallah a bayan wannan limami bayan jifan Maraji’ai da yayi da wannan miyagun lafuzza?

Tambaya daga wasu adadi daga Muminai da Garin Safawi –yankin Hijaz

 

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Yan uwa masa girma Allah kara muku kariyarsa ko wanzu cikin alheri da aminci, daga cikin matsalolin wannan zamani cikin Muminai ma’abota wilaya shi ne ana samun wasu ba’ari suna fadawa cikin wuce gobe da iri ko kuma takaitawa, wannan yana daga cikin alamomin jahilci, lallai ne kamar yanda Sarkin Muminai Ali (a.s) ya fada:

 (الجاهل إما مفرط أو مفرّط)

shi Jahili ko dai wanda ya takaita yayi kasa a gwiwa ko kuma wanda yake wuce goda da iri.

Mutane gama gari shan radadin takaitawarsa da wuce gona da iri, daga cikin raunin da al’umma ke da shi ke sanya su karkata ga mai takaitawa ko kuma mai wuce gona da iri, saboda haka ya zama dole a samar da wayewar kai ga al’umma don gudun kada su fada ga wuce gona da iri da mai takaitawa, shi mafi alherin lamurra shi ne tsakatsakinsu, lallai adalci da falala na cikin tsakatsaki kamar yanda hakan ya tabbata cikin ilimin Aklak, ni akan kin kaina ina yin addu’a ga kaina da dukkanin Muminai maza da mata da shiriya (ka shiryar da mu tafarki madaidaici) ina rokon Allah da ya shiryar da mu baki daya ya gyara lamurranmu ya hade kawukanmu da zukatanmu, lallai mu muna da bukatar hade sahunmu da kauna da soyayya lallai makiyanmu suna murna da sassabawarmu kuma da hakan ne karfin ke raunana mu dinga fasikantar da junanmu, abin da yafi kamata shi ne mu zauna cikin ruwan sanyi mu warware matsalarmu cikin sanya hankali bawai da gaba da juna da yanke yin sallah a bayan juna ba, abin da ya kamata akira wannan limami a tattauna da shi a tsanake da hankalce ma’abita hankali su nusantar da shi zuwa ga abin da alheri ke cikinsa da hade sahu lallai makiya sun araba junanmu domin su shugabance mu, lallai shaidan daga aljanu da mutane yana wurga kiyayya da gaba tsakanimu, ya zama wajibi mu koreshi mu la’ance shi, Allah yana cikin taimakonku, Allah ya dawwamar da ku cikin koshin lafiya.  

Tarihi: [2019/10/17]     Ziyara: [427]

Tura tambaya