mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

jinkirin amsa addu'a

Lallai Allah yana kaunar addu'ar bawansa mumini yana jinkirta amsa masa domin yaji sautinsa:

Lallai Allah yana kaunar addu'ar bawansa mumini yana jinkirta amsa masa domin yaji sautinsa: 

«عن العالم  7: إنّ الله عزّ وجلّ ليؤخّر إجابة المؤمن شوقآ إلى دعائه ويقول : صوتٌ اُحبّ أن أسمعه ، ويعجّل دعاء المنافق ويقول : صوت أكرهه ».

An karbo daga Malami (as): lallai Allah yana jinkirta amsawa bawansa mumini addu'a saboda shaukin addu'ar sa yana cewa: murya ce dana ke son jinta, sannan Allah yana gaggauta addu'ar munafuki, yana cewa: murya ce da bana sonta.[1]

 

عن أمير المؤمنين  7: أحبّ الأعمال إلى الله عزّ وجلّ في الأرض الدعاء.

An karbo daga sarkin muminai (as) mafi soyuwar ayyuka zuwa ga Allah mai girma da daukaka a doran kasa ita ce addu'a.

Ita addu'a cikin kowanne hali kewaye take da taufiki da amsawa ko cikin jinkiri ko kuma cikin gaggawa kamar yadda ya zo daga madaukakin hadisi ita addu'a tana da ladubba da sharudda kamar misalin kyauta zato da Allah da yakini da amsawar sa da larurantuwa zuwa gare shi da tsarkake niyyada shiga ta kofar da Allah madaukaki ya yi umarni da ita, da fuskantar da zuciya zuwa ga Allah, da kaskantar da kai da sirantar da zuciya da daga hannuwa zuwa sama, da farawa da bismillah da girmama Allah da istigfari, da salati ga Muhammad da iyalansa gabanin fara addu'a da bayan idar da ita, da cika alkawari, da cudanya addu'ar da aiki domin ita addu'a tana daga cikin sunnonin Allah, da taruwa wuri daya don yin addu'a da kuma neman mumiani suce amin da sakankancewa cikin addu'a da nema da naci da magiya cikin nema da kiran Allah da sunayensa kyawawa tare da naci

«إنّ الله يحبّ الملحّين في الدعاء».

Lallai shi yana son masu naci cikin addu'a

«إنّ الله يحبّ السائل اللحوح ، ومتى تكثر قرع الباب يفتح لک ».

[1] Wasa'il: m 4 sh 1086

Tarihi: [2019/4/15]     Ziyara: [618]

Tura tambaya