mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Ta yaya zamu iya tabbatar da imamanci Mahadi (Af) da tabbatattun dalilai da yakini

Salamu Alaikum

Ahmad Katib yana cewa imamancin Imam Mahadi (af) bayan Imam Hassan Askari (as) bata tabbatu ba- kuma babu wasu hadisai ko wasiyya daga Askari (as) kan haka, sannan idan ma akwai to raunana ne ba mutawatirai b- ta kaka zamu iya tabbatar da imamancinsa (as) da dalilai na yankan shakku da na yakini.

Haka zalika batun tabbatar imamancin Imam Kazim (as) bayansa Abdullahi Afdahu ya zo, saboda haka ta yaya zamu iya tabbatar imamancin Musal Kazim (as) da tabbatattun dalilai da yakini.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Hakika Hauza ilimiyya tareda manyan malamai sun shelanta cewa Ahmad Katib batacce ne karkatacce mai batarwa, kuma ya ratsewa hanyar gaskiya, saboda haka kada ka saurara daga ratsatstse, ka karbi abinda malamanka na imamiya sukai ittifaki kansa, Allah shine mai shiryarwa zuwa ga daidai, hakika akidunmu gaskiya ne sun tabbatu da dalilalai na yankan  shakku kamar yanda aka ambace su cikin litattafan Kalam, ka neme su ka karanta kamar littafin Akai’idul shi’a da Aka’idul Imamiya da Aslul shi’a wa Usuliha da sauran gomomin litattafai, wannan al’amari ne mai girma cikin imamanci tareda ma’anarsa uku tashri’iyya takwiniya da ijtima’iya, hakika na kawo bayani filla-filla cikin Aka’idul muminin da littafin Addurus fi Usuliddini.

Allah ne mai shiryarwa zuwa madaidaicin tafarki.     

Tarihi: [2019/3/16]     Ziyara: [704]

Tura tambaya