mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Mene ne aljani wanne irin tasiri yake da shi kan mutum

Mene ne aljani wanne irin zurfin tasiri yake da shi kan mutum, shin tasiri ne a ruhi ko kuma na gangar jiki, sannan ya zo cikin fadin Allah madaukaki cikin suratu jinni


Mene ne aljani wanne irin zurfin tasiri yake da shi kan mutum, shin tasiri ne a ruhi ko kuma na gangar jiki, sannan ya zo cikin fadin Allah madaukaki cikin suratu jinni

(رجال من  الانس یعوذون برجال من الجن فازادهم رهقا)

Kuma wasu mazaje daga mutane suna neman tsari daga mazaje daga aljanu sai suka kara musu girman kai.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Shi aljani halitta ce daga halittun Allah kuma shi ma an kallafa masa neman sanin Allah da bauata masa, kamar yanda ya zo cikin fadin Allah madaukaki:

 (ما خلقت الجن والإنس إلّا ليعبدون)

Ban halicci mutum da aljani ba face don su bauta mini.

Kamar yanda yake cikin suratu jinni an kawo kisser aljanu da saurarensu ga kur’ani mai girma, da kuma cewa wasu cikinsu sun yi Imani, ta yiwu wasu daga cikin aljanu suyi tasiri ta hanyar jefa wasiwasi idan aljani ya kasance daga shaidanun aljanu, kamar yanda yana iya yiwa mumini hidima idan ya ksance daga aljanu muminai, kuma ta yiwu su cutawa wanda yake cutar da su, kamar yand aya zo cikin wasu kissoshi da shaidu cewa aljani yana yin tasiri hatta cikin nafsu din mutum sai dai cewa tasiri ne juzu’I ba kulli ba.

Allah ne mafi sani  


Tarihi: [2018/10/2]     Ziyara: [615]

Tura tambaya