mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Shin shaik Muhammad Musa Yakubi da Sayyid Mahmud saraki da Sayyid kamalul haidairi suna daga cikin wadanda ya halasta ayi taklidi da su?

Shin shaik Muhammad Musa Yakubi da Sayyid Mahmud saraki da Sayyid kamalul haidairi suna daga cikin wadanda ya halasta ayi taklidi da su?

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

 

Ka sani kowanne abu yanada ma’auni da mizani da ake sanin lafiyayye daga mara kyawu, da daidai daga kuskure, da gaskiya daga bata, daga kari daga tawaya, domin sanin wadanda ya halasta kayi taklidi da su to lallai ya zo daga imam Hassan Askari (as) cewa : amma wanda ya kasance daga fakihai mai kiyaye addininsa mai katange kansa mai sabawa bin son rai mai biyayya ga umarnin ubangijinsa to amawa suyi taklidi da shi.

Wannan shine mizani ma’aunin ayyana maraji’ai da fakihai, saboda haka ka dora dukkanin mai da’awar marja’iyya kan wannan mizanin kan wannan ma’aunin, babu banbanci cikin kasantuwar mai da’awar marja’iyya daga  shin wadanda hauza ta kyankyashesu ne ko kuma dalibin jami’a ne ko kuma matasa ne masa da’awar marja’iyyar. Matukar dai ka same shi mai katange kansa daga munanan ayyuka da munanan siffofi kamar jiji da kai da ruduwa da ilimi da makamanta haka, saboda shi mai kiyaye addninsa ba zaka sameshi mai fitinuwa da duniyarsa ba, haka ba zaka same shi mai son nuna kansa ba da nuna cewa shi yafi kowa ilimi a malamai, sannan mai sabawa son ransa wannan yana daga cikin abu mai wahalar gaske,  ba a samun irinsu sai cikin daidaiku daga mutane. Sannan mai biyayya ga umarnin ubangijinsa ba umarni wane da wane ba, ba kuma mai bin rai mai umarni da mummuna ba.

Idan ka samu wannan to ya halasta kayi taklidi da shi kuma yin taklidi da shi na sauke nauyin shari’a, sannan duk wanda bai kasance da wadannan kyawawan siffofi ba to kawai ka sanya cikin kwandon sharar mantattu.

Lallai yadda al’amarin yake shine ba zaka taba samun canji  ciokin sunnar Allah ba.

Allah ne abin neman taimako shine kuma mai shiryarwa zuwa daidai, dacewarmu da damdagatar dinmu na wurin Allah masani mai girma, sannan babu tsimi babu dabara face da Allah madaukaki mai girma, karshen maganarmu dukkanin godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki. 

Tarihi: [2018/2/3]     Ziyara: [915]

Tura tambaya