mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Ya halasta a aske gemu gabanin cikar kwanaki arba’in daga zaman makokin mamaci?

Salamu Alaikum
Shin Ya halasta a aske gemu agabanin cikar arba’in din mamaci?

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

 

Lallai sh’anin mutane nada ban mamaki lallai al’amarin yadda yake shi ne kamar yadda manzon Allah (s.a.w) yake cewa :

بسم الله الرحمن الرحیم

يأتي زمان على الناس يكون المعروف منكراً والمنكر معروفاً،

Wani zamani zai zo kan mutane da kyakkyawan abu zai wayi gari munkari sannan munkari zai wayi gari kyakkyawa.

Ka sani cewa shi aske gemu ta kowacce fuska haramun ne, abin ban mamaki daga mutane lokacin da ake musu bayanin haramcin aske gemu sai ka same su suna cewa idan bamu aske gemu zamu dinga fama da kaikayi a kan habarmu, sai dai cewa ni ban sani to menene kuma ya sanya su lokacin da wani dan’uwansu ya mutu sai su bar gemu suki aske shi har tsawon kwanaki arba’in to yanzu kuma ina maganar kaikayin da suke ji ta kwana ?! yanzu anyi gari ba a bin umarnin Allah sai umarnin al’adu, domin a al’adar mutane suna ganin daya daga cikin hanyar bayyana bakin ciki ga mamaci shi nekada su aske gemunsu, ya subhanallah sai munkari ya zama abu mai kyau shi kuma bu mai kyau ya wayi gari munkari.

Ya kai mai tambaya ka sani aske gemu ta kowacce fuska bai halasta ba mudlakan babu banbanci kafin mutuwar dan’uwanka ne ko bayanta, ina rokar Allah majibancinka dani da dukkanin shi’ar Alu Muhammad da shiryar damu da shiriya da ma’arifa da sanin halal da haram da aiki managarci amin amin.  

Tarihi: [2018/3/10]     Ziyara: [697]

Tura tambaya