mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Shin wannan riwayar ta inganta

Salamu Alaikum
Riwaya ta zo kamar haka: ya zo cikin littafin Aljunnatul Aman cewa wani mutum ya zo wajen Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi da iyalansa, sai yace ya Manzon Allah (s.a.w) ni na kasance Mawadaci sai na talauce, na kasance mai koshin lafiya sai na fada cikin rashin lafiya

Salamu Alaikum
Riwaya ta zo kamar haka: ya zo cikin littafin Aljunnatul Aman cewa wani mutum ya zo wajen Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi da iyalansa, sai yace ya Manzon Allah (s.a.w) ni na kasance Mawadaci sai na talauce, na kasance mai koshin lafiya sai na fada cikin rashin lafiya, na kasance mai farin jini cikin mutane sai na zama abin kyama, na kasance mai saukin nauyi kan zukatansu sai na zama mai nauyi, na kasance cikin farin ciki sai damuwa kala-kala ta tattaru a kaina, hakika Kasa ta kuntace a kaina tareda yalwarta ina yawo tsawon yinina cikin neman arziki ban samun abinda zanci a yini, kai kace sunana an shafe shi daga diwanin da aka dawwana arzuka, sai Annabi (s. a.w) yace masa ta yiwu kana aikata abubuwan da suke motsar da bakin ciki, sai mutumin yace wadanne abubuwa ne suke motsar da bakin ciki, sai ya cewa mutumin ta yiwu kana daura rawani a tsugune, ko kuma kana shafa fuskarka da jelar  riga, mo kuma ka hin bawali cikin kududdufi, ko kuma kana kwanciya rufda ciki. 
Shin wannan riwaya ta inganta idan ta inganta hakan nufin idan mutum bai aikata wadannan abubuwa ba bakin ciki zai yaye daga barinsa. 
ina neman karin bayani. 
 
da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai
ya wadatar cikin mustahabbat mo kuma cikin Makarubai riko da madogarar saukakawa cikin dalilan sunna kamar yadda wannan shi ne ra'ayin da muka zaba sabida haka ya halasta yin aiki da wannan riwaya, 
kuma lallai su Kaziyoyi ne da suka zo da harshen Kaziya Muhmala bawai Sura ga baki dayan kowanne kaziya ba kamar yanda bayanin hakan yake a ilimin Mandik da har hukuncinta zai zama yana tattaro kowanne fage ba. 
Allah ne mafi sani

Tarihi: [2020/4/17]     Ziyara: [399]

Tura tambaya