b SHIN ZAMU SAMU WANI WURIDI DAGA GAREKU DOMIN BUDE KOFOFIN DUNIYA DA LAHIRA
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

SHIN ZAMU SAMU WANI WURIDI DAGA GAREKU DOMIN BUDE KOFOFIN DUNIYA DA LAHIRA

Salamu Alaikum warahmatullahi wa barakatuhu Allah ya karbi ayyukanku da da’arku
Ya zo daga Sarkin Muminai Ali (a.s) yana cewa: na ga Kidir a mafarki gabanin yakin Badar da kwana daya sai na ce masa sanar da wani abu da zan yi galaba kan makiya sai yace masa ka karanta (ya huwa ya man lahuwa illa huwa).

Yayin da na wayi gari sai na gayawa manzon Allah (s.a.w) abinda ya faru sai yace: ya Ali ka samu sanin Ismul A’azam, wannan suna ya kasance ranar yakin Badar a kan harshena.

Tambayar farko: menene ingancin wannan hadisi?

Tambaya ta biyu: ku taimaka mana da wani wuridi zamu bude kofofin duniya da lahira da shi?

Ku fa’idantar da mu Allah ya saka muku da alheri.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Kalmar la’ilaha illallahu shingen Allah ce kuma duk wanda ya shiga shinge ne ya aminta daga azabar Allah duniya da lahira amma fa tareda sharadi da sharuddanta daga cikin sharuddanta Imamanci daga cikin sharuddanta Iklasi  duk wanda ya fadi wannan Kalmar cikin tsarkake niyya aljanna ta wajaba kansa , sannan alamar iklasi shi ne tsantseni  daga barin ayyukan haramun, ya zama dole a kiyaye tak’wa mafi karancin tak’wa shi ne sauke wajibai da kauracewa haramun.

Wurin Allah ake neman taimako.

Tarihi: [2019/11/27]     Ziyara: [638]

Tura tambaya