mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Shin zamu iya tura `ya`yanmu makarantun wahabiyawa wadanda tsarin koyarwarsu ke kan akidun wahabiyanci

Salam Alaikum. Sayyid ina fatan zan samu gamsashiyyar amsa filla-filla gwargwadon iko kan wannan mas’ala mai zuwa: makarantun gwamnati a kasashenmu suna kan tsarin koyarwar wahabiyancim tun bayan bullowar wadannan makarantu al’umma suka kasu kahsi biyu, kashi guda na goyon bayan hukuma daya kason kuma ya bijirewa wannan tsari, sai dai cewa daga bayan kason farko yayi ta raguwa har suka wayi gari tsiraru, daya kason kuma masu goyon baya suna tura yaransu makarantun basa ganin kowacce irin matasala cikin halin katanguwa yaro daga cutuwa bisa dogaransu da fatawowin maraji’ansu, suna cewa fatawowin maraji’ai sun kasance kamar haka: daga cikin maraji’ai akwai wanda yake ganin halascin karatu cikin wadannan makarantu bisa cikar sharudda larurar katange yaro, daga cikinsu akwai wadanda suka tafi kan cikar sharudda kan yra maza kadai ban da mata da haramci mudlaki ga yara mata, kaso na karshe daga cikinsu sune wadanda suka haramta mudlakan sun kuma sabawa kason farko da hujjoji kamar haka: cewa ana koyar da darussan addini cikin wadannan makarantu kan tsarin wahabiyanci karkatacce saboda haka yaro na iya samun gurbatar akidarsa.

Cikin tsarin koyarwarsu akwai izgilanci ga ayoyin Allah ta fuskanin kafirta Abu dalib (as) da kafirta mahaifan manzon Allah (s.a.w) da kuma nuna shakku kan kyawawan dabi’unsa da sukansa.

Babu wand azia kai `ya`yansa wannan makaranta sai mara kishin annabinsa da A’imma (as) cikin haka daidai yake da wanda ya mika dansa ga Yazidu bn Mu’awiya.

Lallai cikin turasu wannan makarantu akwai barazanar gurbatar dabi’unsu cikin cudanyarsu da gurbatattun dalibai da malamai.

Babu wata larura cikin turasu can, ko da kuwa shaida kammala karatu itace kadai hanyar samun aikin yi a wannan zamani, shi Allah ne mai azurtawa, mumini zai iya yin aiki mai cin gahsin kansa misalin kasuwanci maimakon ayyukan hukuma.

Cikin wannan mas’ala mumini bai bukatar neman fatawar Marja’i domin karfafa da nunar hankali ya isar cikin gano haramci, aiki da fatawar maraji’ai cikin wannan hali bai sauke nauyi daga wuya. Suna kafa hujja kan haramcin da wananan aya mai albarka

(وَقَدْ نَزَّلَ عَلَيْكُمْ فِي الْكِتَابِ أَنْ إِذَا سَمِعْتُمْ آيَاتِ اللّهِ يُكَفَرُ بِهَا وَيُسْتَهْزَأُ بِهَا فَلاَ تَقْعُدُواْ مَعَهُمْ حَتَّى يَخُوضُواْ فِي حَدِيثٍ غَيْرِهِ إِنَّكُمْ إِذاً مِّثْلُهُمْ إِنَّ اللّهَ جَامِعُ الْمُنَافِقِينَ وَالْكَافِرِينَ فِي جَهَنَّمَ جَمِيعاً

Hakika mun saukar muku cikin littafi idan kuka ana kafircewa ayoyin Allah ana musu izgilanci to kada ku zauna tareda su har zai sun canza Magana.

Hakama ya zo cikin fadinsa madaukaki:

(وَإِذَا رَأَيْتَ الَّذِينَ يَخُوضُونَ فِي آيَاتِنَا فَأَعْرِضْ عَنْهُمْ حَتَّى يَخُوضُوا فِي حَدِيثٍ غَيْرِهِ وَإِمَّا يُنسِيَنَّكَ الشَّيْطَانُ فَلا تَقْعُدْ بَعْدَ الذِّكْرَى مَعَ الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ

Idan kaga wadanda suke kutsawa cikin ayoyinmu ka kaurace musu har sai sun kutsa cikin wata Magana daban idan shaidan ya mantar dakai kada ka zauna tareda azzalumai bayan tunawarka.

Tambaya a take fadowa kwakwalwa shine shin wannan ishkaloli da suke gangaro dasu suna zama hujj? Shin ana la’akari da su cikin ma’aunin fikhu?

Shin fakihai basu karanta wadannan ayoyi guda biyu ko kuma sun karanta su amma su gaza fahimtar abinda wadannan suka fahimta?

Tsokaci:

A shekarar 2006 na samu damar ganawa da Marja’I Ayatullah Wahidul Kurasani  na tambaye shi kan wannan mas’ala sai ya bani amsa da cewa: ya halasta bisa cikar sharuddan larura da katange yaro, sannan ya kara da cewa yaku `ya`yana ku zage dantse ku dage kada kuyi sakaci wahabiyawa su gabaceku.

Sai dai cewa sakamakon amsar baki da baki ya gaya mini ba a rubuce ba sai na gaza gamsar da masu ra’ayin haramtawa.

Sau da yawa mu kan aiko da tambaya zuwa ofsihinsa sai dai cewa bamu samun amsa.

Da sunaN Allah mai rahama mai jin kai

Kamar yanda ake cewa( Makka tafi kowa sanin mutanenta) mazauna kowanne gari cikin bayyanar da masadik din maudu’ai sunne mafi sani daga waninsu, sai dai cewa kafa hujja da wadancan ayoyi biyu kadai ya inganta ne ga wanda ya kasance Mujtahidi wanda ya cika sharudda, domin fatawa da hukunci basu dogara kadai da littafin Allah bari dai akwai riwayoyi da ijma’i da mustakillat akliya da wasunsu daga dalilan nakali, yafi cancanta da dacewa ga wadannan kamar yanda baban buga misali yake cewa: ( ka barta a wuyan malami ka fita daga cikinta lafiya)

Ma’auni shine fatawar maraji’ai cikin zamanin gaiba Kubra domin kowanne guda da kansa yana kafa hujja da aya da riwayoyi cikin hukunce-hukuncen shari’a kamar haramci wajabci, na’am cikin zayyane maudu’i idan Allah bai zayyana shi ba to a wannan hali ana komawa ga mazauna wannan muhalli.

Allah ne mai bada kariya

بسم الله الرحمن الرحیم
Tarihi: [2019/3/4]     Ziyara: [564]

Tura tambaya