mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Hukuncin istimna’i?

Slm: na kasance ina aikata wannan istimna’i kuma nasan babu kyau dalili kuwa inason in bari, amma na kasa to shine nake son insan hukuncina?

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Galabar sha’awar jinsi cikin abubuwan da aka haramta kamar misalin istimna’i ga wanda ya kasance bai da aure, to wajibi ne kansa ya ji tsoran Allah kamar yadda ya zo cikin hadisi:

اتقوا معاصي الله في الخلوات ، فإن الشاهد هو الحاكم

 kuji tsoraN cikin halwowi lallai mai gani shine mai hukunci.

Ba zai yiwu a gujewa hukmarsa ba kamar yadda ya zo cikin du’a’u kumail, kamar yadda ya kamaceka ka dinga tunawa da mutuwa sosai dukkanin wanda ya tuna da mutuwa sau ashirin cikin kowacce rana lallai hakan za a bashi ladan shahidai, za kuma rubuta shahidi, saboda haka kowacce rana ka dinga tuna mai rusa jin dadi da sha’awe-sha’awe wacce ita ce mutuwa da sharadin kada ka kai zuwa ga haddin debe tsammani rayuwa.

Kamar yadda ya kamceka ka ziyartar kaburbura ko da dai sau daya ne a cikin kowanne sati ka dinga tuna halin matattu dake kwance cikin kabari da cewa lallai wata rana sun kasance raye kamar kai. Suma sha’awa tana galaba kansu suka sabawa Allah ga shi yau kuma suna karkashin turbaya suna hannun Allah to me zasu cewa Allah?

Sannan ya zama wajibi gareka kai abota da mutanen kirki kayi watsi da ashararan abokai.

Haka ya kamaceka ka yawaita karanta littatafan Akhlak da addini da rayuwar annabawa da kissoshinsu da tarihin bayin Allah nagargaru salihai da A’imma tsarkaka amincin Allah ya kara tabbata garesu.

Allah ne abin neman taimako
Tarihi: [2018/2/10]     Ziyara: [1125]

Tura tambaya