b Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar haihuwar imam mai tausayi sarki aliyu ibn musa arrida amincin Allah ya tabbata gare shi
sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
  • Laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye cikin dandali sadar da zumunci na Instagram
  • Muhadarorin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Ramadan Mai albarka a shekara ta 1442 hijiri
  • Allah ya farantawa kwanakinmu da naku, muna farin cikin nuna murna da farin ciki ga al’umma musulmi shi’a da sunna kan haihuwar Imam Mahadi
  • MUNA TAYA KU MURNAR TUNAWA DA RANAR HAIHUWAR IMAM HUSAINI A.S
  • Allah ya faranta kwanakinku da namu cikin tunawa da ranar da aka aiko da Annabi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar kofar samun biyan bukatu Imam Musa Alkazim (A.S)
  • muna taya gurguzun al’ummar musulmi murnar zagayiwar ranar haihuwar Sarkin Muminai Aliyu BN Abu Talib amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
  • Sabon littafi mai suna (Ruhul Inaba fi Tafsiril Du’a Sari’ul Ijaba) wallafar Samahatus Assayid Adil-Alawi
  • Ubangiji ya faranta kwanakinku bisa zagayowar ranar haihu war Assayada Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta
  • Munasabar tunawa da nasarar juyin juya halin muslunci a cikin Iran
  • Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
  • Shahadar Fatima Azzahra A.S
  • Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
  • Muna taya daukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar Mauludin Annabi (s.a.w) da jikansa Imam Jafar Assadik (a.s)
  • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Hassan Askari amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da wafatin Manzon Allah (s.a.w) da kuma shahadar jikokinsa Imam Hassan Almujtaba da Imam Rida (a.s
  • Allah ya grimama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Hassan Almujtaba amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa shahadar Imam Sajjad (a.s)
  • sababun labare

    Labarun da ba tsammani

    Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar haihuwar imam mai tausayi sarki aliyu ibn musa arrida amincin Allah ya tabbata gare shi


    Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar haihuwar imam mai tausayi sarki aliyu ibn musa arrida amincin Allah ya tabbata gare shi



    wani `dan kwarface da kamface daga tekun kyawawan dabi’un imam rida (as) tare da alkalmin sayyid adil alawi.

    Daga cikin kyawawn sirar imam rida (as) tare da sahabbansa da shi’ar kakansa amirul muminina aliyu ibn abi dalib amincin Allah ya tabbata gare shi ta yadda ya kasance ya na tarbiyantardasu da kwadaitar da su kan lazimtar farillan addini, da kwabarsu da hansu yin sakaci da sako-sako da hakkokin ragowar mutane.

    Alal misali ya zo cikin littafin al’ihtijaj na malam dabarasi da isnadinsa ya ce: lokacin da aka nada ali ibn musa arrida (as) sarautar mai jiran gado wani hadiminsa yaje wajensa – sai ya ce masa: hakika wasu mutane suna bakin kofa tsaye suna neman izinin shigowa suna fadin cewa su yan shi’arka kakanka aliyu ibn abi dalib (as) sai imam rida amincin Allah ya tabbata gare shi ya ce: ina da aiki ka sallame su su tafi, sai wannan hadimi yaje ya sallame su suka tafi.

    ya yinda rana ta biyu ta kasance sai suka kara zuwa sai ya kara nema musu izinin shiga suka kara cewa su `yan shi’ar ali ibn abi dalib kakansa (as) ne, sai imam (as) ya maimaita abin da ya gaya musu a ranar farko sukai ta zuwa suna maimaita haka shima ya maimata musu haka har ya tawon watanni biyu, daga karshe suka debe tsammanin ganin imam rida (as) suka cewa hadiminsa: ka gayawa shugabanmu lallai mu shi’ar babansa ne ali ibn abi dalib amincin Allah ya tabbata gare shi, hakika makiyanmu sun mana dariya cikin shingen da ka saka tsakaninmu da kai, lallai wannan karon ma zamu kara komawa, zamu gudu daga garinmu saboda tsananin jin kunya da kuma bisa `dagewar abin da muke gani ya riske mu, da kuma gazawa daga jure radadin abin da zai faru damu ya riske mu daga dariyar da makiyanmu za su yi mana.

    Sai imam aliyu ibn musa arrida (as) ya ce: kai musu izini su shigo, sai suka shiga wajen imam (as) suka ce ya `dan manzon Allah me ya kawo irin wannan jafa’i haka mai girma da wulakanci bayan wannan hijabi mai tsanani haka? wacce mai raguwa ce za ta ragu daga garemu bayan wannan?    

    Sai imam rida (as) ya ce: ku karanta fadin Allah madaukaki:

    Duk abin da ya same ku daga musiba daga abin da hannayenku ta tsiwirwira yake* ya na kuma afuwa daga yawa-yawa.

    Imam ya ce banyi koyi cikinku ba face da ubangijina mai girma da daukaka, da kuma manzon Allah amincin Allah ya tabbata gare shi da mutanen gidansa da kuma amirul mumina amincin Allah ya tabbata gare shi bayansa kuma iayayena tsarkaka lallai dukkaninsu sun zargeku sai nima nayi koyo da su.

    sai suka ce saboda menene ya `dan manzon Allah (s.a.w) ?

    Ya ce : sakamakon da’awar da ku kai ta cewa ku kuna daga `yan shi’ar amirul mumina aliyu ibn dalib amincin Allah ya tabbata gare shi, kaiconku kadai dai `yan shi’arsa sune hassan da husaini da salmanu da abu zar da mikdadu da ammar da muhammadu ibn abubakar  wadanda basu taba sabawa wani abu daga umarninsa ba, ba su taba aikata wani abu daga abubuwa da ya kwabesu kai ba, amma ku idan ku kace kuna daga shi’arsa alhalin ku kuna saba ma umarninsa cikin mafi yawan ayyukanku, kuna takaitawa cikin da yawa-yawan farillai, kuna sakaci cikin girman hakkokin `yan’uwanku cikin Allah, kuna yin takiyya a wuraren da ita takiyyar ba wajibi ba ce, kuna barin aiki da takiyya a lokacin da takiyya ta ke wajibi, da dai kun ce ku masoyansa ne masu kaunarsa masu kaunar masoyansa masu kiyayya da makiyansa da ba zan yi musun fadinku ba, sai dai cewa kunyi da’awar babban matsayi, duk da kasantuwar baku gasgata fadinku da akinku ba, sai dai kawai rahama daga ubangijinku ta riskeku.

    sai suka ce : ya `dan manzon Allah lallai mu muna neman gafarar Allah muna tuba zuwa gare shi daga wannan furuci namu, bari dai zamu dinga fadi kamar yadda ka koya mana ya shugabanmu, mu masoyanku ne masoyan masoyanku makiyan makiyanku.

    Sai imam rida (as) ya ce : maraba da ku ya `yan’uwana ma’abota kaunata, ku daukaka ku daukaka bai gushe ba ya na ta daukaka darajarsu har sai da ya manna su da kansa, ya binciki al’amarinsu da al’amarin iyalansu, ya basu kyauta mai tarin yawa ya yalwata su da ita.

    Ina cewa wannan hadisi madaukaki ya na dauke da darasussuka masu `kima da amfani, da zamu shiga bayaninsu filla-filla da hakan ya wajabta mana tanadar littafi da mujalladi masu tarin yawa, sai dai cewa zamu yi ishara a takaice gwargwadon fahimtarmu zuwa ga jumla daga hadisin kamar jagaban alkaluma mu sallama ragowar neman bayanin filla-filla ga kaifin basirar mai karatu  mai girma da fadakarsa da wayewarsa ta ilimi, daga cikin darussan da hadisin ke dauke dasu shi ne:

    1- ya kamata a fara neman izinin shiga, cikin hakan kuwa babu banbanci ga wanda yake ziyartar imami a zamani da yake raye da wanda ke ziyartarsa a kabarinsa, saboda gamewa al’amarin da kuma abin da mu kai imani da shi a makarantar kur’ani mai girma da ahlul-baiti: daga rayuwarsu ta barzahu kamar rayuwar shahidai  wurin Allah madaukaki: (su rayayyu ne suna azurtuwa wajen ubangijinsu)

    2- ya kamata ya zamnto anyi alkawalin ganawar gabaninta duk wanda ya zo ziyara ba tare da amma sa alkawalin ganawa da shi ba tun baya ba, ba a kuma yi masa izini ba, sau da yawan lokaci yana iya haduwa da uzuri ya zamanto ba ai maraba da shi ba.

    3- hakika masoyi mai kauna baya kosawa daga haduwa da masoyinsa ko da kuwa hadu da kora da saddu daga masoyinsa, sai ka sameshi ya na zuwa kowacce rana ko da kuwa bai samu biyan bukatarsa ba.

    4- ya na da tsananin wahala mutum ya jurewa dariyar makiya, tabbas makiya masoyan ahli-baiti suna nuna kiyayarsu garesu, suna kuma yi musu dariya idan wata musiba ta same su, tabbas imamai : suna fahimatar ma’anar wannan ga masoyansu suna kuma girmama irin wannan yanayi da suke ciki mai tsanani da kuma wahala, kamar yadda imam rida (as) daga karshe ya yi musu izinin shiga.

    5- dole ne a mayar da dukkanin al’uma zuwa ga kur’ani su kuma kasance suna dabbaka rayuwa kan haskensa kamar yadda imam rida (as) ya kafa dalili da shi.

    6- na farkon wanda ake koyi da shi shi ne Allah matsarkaki ubangijin talikai, tabbas ana koyi ne da mai bada tarbiya, ta yiwu imam (as) ya zabi wannan suna mai daukaka (ubangijina) domin ya zamanto ishara zuwa ga wannan ma’ana cikin al’umma don su san na farkon wanda zai zame musu abin koyi shi ne ubangiji, sannan na biyu shi ne manzon Allah amincin Allah ya tabbata gare shi   

     (ولكم في رسول الله اسوة حسنة )

    Tabbas kuna da abin koyi mai kyawu cikin manzon Allah.

    Sannan amirul muminin aliyu ibn abi dalib (as) da imamai tsarkaka daga mutanen gidansa, tabbas sune hakikanin muhammadiya abin koyi ga dukkanin mutane baki daya.

     7- zargi yana halasta idan ya kasance daga tushen tarbiyya da koyarwa kadai dai zargi daga wanda ya kasance daga ahalinsa daidaita tsakanin imamai da al’umma, idanh ko baha ka tabbas hakika duk wanda zarginsa ya yawaita abokansa zasu karanta.

    8- abin da ya fi dacewa shi ne kowanne mutum ya yi da’awar gwargwadon abin da yake da shi.

    9 shi’anci duk da kasantuwarsa da ma’anar gamammiya a tarihi da kungiyoyin musulunci na dabbakuwa kan dukkanin wanda yake raya da Imani da halifancin amirul muminina ali ibn abi dalib (as) bayan manzon Allah (s.a.w) ba tare da yankewa ba, sai dai cewa yadda al’amarin yake wurin dukkanin shi’a, shi ne sune kungiya kubutacciya wadda ta tsira daga halaka wadanda sukai imani da imamai goma sha biyu (as): na farkonsu amirul muminina ali (as) na karshensu sahibuz zaman almahadi daga mutanen muhammadu (s.a.w) amma shi’a da kebantaccciyar ma’ana sune misalin salmanu da abu zar, sannan shi’a da mafi kebantar ma’ana sune kamar misalin annabi Ibrahim masoyin Allah (as) da Hassan da husaini (as) da mala’iku ma’asumai, imam amincin Allah ya tabbata gare shi abin da ya yi nufin yin ishara zuwa gare shi shi ne `da shi’a mai gaskiya cikin abin da yake da’awa  kai, kamar misalin `yan shi’a cikin kebanta da cikin mafi kebanta, kamar yadda ya buga misali da wadannan zababbu na farko farko daga rabautattun shi’a, wadanda ya siffanata su da cewa su basu sabawa wani abu daga umarnin shugabansu imaminsu amirul mumina ali (as) haka basu gangancin zakkewa wani abu daga abubuwan da ya hanesu, wannan ya kasance kamar misalin rular da ake jan mikakke layi da karkatacce kan takarda da ita.

    10- dukkanin da’awa dole ta kasance tanada wani shaida da dalili da yake nuni zuwa gaskiyarta, duk wanda ke da’awa cewa shi `dan shi’a ne to dalilinsa da shaidarsa kan hakan shi ne ayyukansa da zantukansa su kasance daidai da umarni da hanin shugabansa da haninsa da tsawatarwarsa basu sabani, amma idan ya kasance aikinsa bai gasgata maganarsa, to wannan ba mai gaskiya bane cikin abin da yake da’awa, da’awarsa ba ta daidai da hakikar da ta ke waje da ainahin al’amari, tabbas labarin gaskiya shi ne wanda ya kasance ya na daidaita da hakikanin da abin da ake gani a fili da sararinsa bawai abin da mai Magana ke rayawa ba, kamar yadda aka ambaci haka a muhallinsa.

    11- imam amincin Allah ya tabbata gare shi ya na ishara ya zuwa ba’arin wasu munanan ayyuka da zantuka, daga wanda yake da’awar cewa shi shi’ar amirul mumini ne da kasantuwarsa ya na sabawa shugabansa cikin mafi yawa-yawan ayyukansa, da kuma kasantuwarsa ya na kasa agwiwa da gazawa cikin farillai, zaka ganshi baya yin sallah sai dai gurbatacciyar sallah cikin wargi da sakarci, ya na caccake kamar caccaken tsuntsu, ya na wasa da tufafinsa cikin sallah zuciyarsa bata kushu’i, yana tunanance tunance duniya, sai ka same shi yana halarto da abubuwa da ya manta shi yana tareda komai sai dai sallah ce kadai a baya, wannan duk a cikin farillai kenan za kuma ka same shi mai sakaci da hakkokin `yan’uwansa muslmai daga masoya masu kauna da biyayyar mazhabar ahlul-baiti (as) lallai kan mumini akwai hakkoki saba’in kamar yadda ya zo cikin hadisai, sannan imani da takiya suna daga jigon mazhabar ahlul baiti sai dai cewa wasu ba’ari basu san yanda ake amfani da takiyya ba, ba kuma su san wurin da ake aiki da ita ba, da wanda ake yiwa takiyyar ba da ma wurin da samsam ba ta ma wajaba ba, wannan kuskuren da ire irensa zaka samu masoya ahlul baityi (as) na tafka shi kowacce rana, daga na kuma zaa  kiyasta shi a wani wurin daban.

    12- sannan bayan wannan Karin haske na imam rida da fairar alawiya, imam ya na koyawa mabiyansa masoya wadanda suka jurewa wahalhalun tafiya suka taho ziyartarsa suka tsaya bakin kofarsa har tsawon watanni biyu cikin radadin juriyar dariya da izgilin makiyansu, yadda al’amarin yake shi ne ka da ku furta abin da bai tabbata cikinku ba na fadin cewa ku `yan shi’ar amirul mumini ne, bari dai ku fadi hakikanin abin da ke cikinku daga kasantuwarku daga masoyansa amincin Allah ya tabbata gare shi, sannan ya zama tilas ku kasance tare da wilaya da bara’a, dukkanin wanda ya kasance masoyinsa (as) to ya zama tilas a same shi ya na kiyayya da makiyansa (as) idan kuma ba haka ba to zai kasance kamar yadda amincin Allah ya tabbata gare shi yake fadi:       

     (عجبت لمن يدعي حبي كيف يحب عدوي )

    Ina mamakin wanda ke da’awar cewa shi masoyina ne ta `ka`ka zai dinga son makiya na.

    Haka ma ya zo cikin ingantattun hadisai fadinsa (as)

     (كذب إنه يحبّنا ولم يبغض عدونا)

    Karya yake wanda yake raya cewa shi masoyinmu ne alhalin bai nuna kiyayya ga makiyinmu.

    13-Hakika shi`anci da `yan shi’ar amirul muminina matsayi ne madaukaki a wurin Allah da manzon Allah da imamai tsarkaka.

    14- halaka ga wanda ya kasance munafuki wanda shi ne zahirinsa ke sabawa da badininsa, furucinsa bai dacewa da aikinsa.  

     (لِمَ تقولون ما لا تفعلون )

    Me yasa kuke fadin abin da bakwa aikatawa.

    Ya zama tilas a samu gasgatuwar furuci ta hanyar aikata shi ma’ana aiki da abin da ke fada, idan ko ba haka zai kasance cikin halakar duniya da lahira, matukar dai aikinku bai daidaita ya gasgata da abin da kuke fada ba kun halaka..

    tabbas rahamar Allah tana yalwata mumini kada ya debe tsammani daga rahamar Allah, ya dai kasance cikin kowanne yanayi ya na sa ran rahamar za ta riske shi.

    16- ikirari da kuskure daraja ce mai girma, kamar yadda annabi adamu ya yi ikirari da kuskurensa Allah ya karbi tubansa ya sanya shi cikin aljanna ya komar da shi hallararsa matsarkakiya, tabbas Allah ya na karbar tuba ya na gafarta zunubai ga dukkanin wanda ya tuba zuwa gare shi ya kuma yi imani ya aikata aiki nagari sannan ya yi riko da shiriya, tabbas Allah zai gyara al’amarinsa.

    17- masoyi cikin furucinsa da ayyukansa ya na biyayya ga waliyyansa, ya na karba daga iliminsu da rike su gam.

    18- duk wanda ya so wanda Allah yake so da manzonsa tabbas Allah matsarkaki ya na son shi, haka al’amarin yake ga wanda ya so abin da sunan Allah ke kansa, tabbas hakan ya na daga cikin soyayyar Allah kamar yadda ya zo cikin munajatin imam aliyu zainul abidin (as)  

    «اللّهم أرزقني حبّک وحبّ من يحبّک وحبّ كلّ عمل يوصلني إلى قربک »

    ya Allah ina rokonka da ka azurta ni da sonka da son wanda yake sonka da son dukkanin wani aiki da zai kai ni zuwa gareka.

    Dukkanin aanda ya so imamai tabbas shi babu shakka zai so shi’arsu da masoyansu masu kaunarsu zai kuma ki dukkanin makiyansu sakamakon lazimtuwa tsakanin wilaya da bara’a.

    19- son imamai tsarkaka da jebantarsu da yi musu biyayya falala ce daga nmukami mai girma da yake janyo `yan’uwatakar imamai, mutum ya kasance daga ma’abota kaunarsu, sai soyayya ta kasance tana jujjuyawa tsakanin bawa da mai gidansa, mai yafi girma daga wannan matsayi me yafi shi kayatarwa da kyawunta, tabbas ita wannan soyayya tana kawo abokantaka sannan ita abokantaka matsayi matsayi ce,

     (يرفع الله الذين آمنوا منكم والذين أُوتوا العلم درجات )

    Allah yana daukaka darajar wadanda sukai imani da wadada aka baiwa ilim.

    darajar bawa bata gushe ba tana daukaka sakamakon soyayyar da yake yiwa imaminsa waliyinsa ma’asumi  (as) har sai ta jingine zuwa jikinsa ya kasance cikin irin darajarsu a cikin matsuguno wajen sarki ma’abocin kudura da iko, kamar yadda ya zo cikin ziyararsu kamar yadda bayani ya gabata.

    20- imam amincin Allah ya tabbata gare shi shi mabayya na ce daga mabayyanun sunayen Allah da rahamarsa mayalwaciya, idan bawa ya yi ikiririn kuskrensa ya tuba zuwa ga Allah, tabbas Allah zai karbi tubansa, zai faranta masa zai kusanto shi zuwa gare shi, zai biya masa bukatunsa, haka al’amarin yake ga imam (as) lallai shi madubi ne na sunayen Allah da sifofinsa, tabbas imam mai jin kai aliyu ibn musa arrida daga mutanen gidan Muhammad lokacin da ya karbi tuban wadannan sahabban nasa wadanda  suka tsaya bakin kofar gidansa suna neman izini shiga wurinsa tsawon kwanaki da watanni suna tsimayin tausayinsa da jin kansa domin basu damar shiga farfajiyar rahamarsa, suka tuba zuwa ga Allah natsarkaki daga furucinsu da da’awarsu suka dawo sukai gyara furucinsu kamar yadda imaminsu ya gyara musu, tabbas shi amincin Allah ya tabbata gare shi ya yi maraba da su ya zanta da su ya kira su da mafi kyawun kalma data nuni zuwa ga soyayya da girmamawa cikin fadinsa:

     (يا اخواني وأهل ودّي )

    ya `yan’uwana ma’abota kaunata.

    Sannan ya umarce da daukakada daukakaya kuma kusanto su jikinsa, bai gushe ba ya na ta yin haka har sai da ya likasu jikinsa, ya tsugunar da su kusa da shi, bawa ya kasance tare da mai gidansa a cikin matsayi a majalisi guda?!!

    Sanna ya duba al’amarinsu da al’amarin iyalansu ya cika su da kyauta, wannan wani darasi ne mai girma ga wanda ya kasance kan matsayin jagoranci da shugabanci da imamanci, ace ya tsaya ya na bibiyar halin wanda yake shugabanta ya dinga tambayar halin da suke rayuwa ya mika musu hannun taimakonsu da iyalansu ya kuma dinga yalwata su da kyaututtuka, ma’ana wani lokaci zai basu taimako da sunan kasantuwarsa ubangidansu da ya zama wajibi ya ciyar da su, wani karon kuma da sunan ihsani da kyautatawa, wani lokacin kuma zai basu da sunan yalwata musu cikin ciyarwa, cikin kowacce kalma na nuni da tausasawa da tarin hakika wacce ahalinta ke tsinkaya, wannan kadan kenan daga abubuwan da wannan hadisi ya kunsa.