sababun labare
- Labarai » Laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye cikin dandali sadar da zumunci na Instagram
- Labarai » Muhadarorin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Ramadan Mai albarka a shekara ta 1442 hijiri
- Labarai » Allah ya farantawa kwanakinmu da naku, muna farin cikin nuna murna da farin ciki ga al’umma musulmi shi’a da sunna kan haihuwar Imam Mahadi
- Labarai » MUNA TAYA KU MURNAR TUNAWA DA RANAR HAIHUWAR IMAM HUSAINI A.S
- Labarai » Allah ya faranta kwanakinku da namu cikin tunawa da ranar da aka aiko da Annabi
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar kofar samun biyan bukatu Imam Musa Alkazim (A.S)
- Labarai » muna taya gurguzun al’ummar musulmi murnar zagayiwar ranar haihuwar Sarkin Muminai Aliyu BN Abu Talib amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
- Labarai » Sabon littafi mai suna (Ruhul Inaba fi Tafsiril Du’a Sari’ul Ijaba) wallafar Samahatus Assayid Adil-Alawi
- Labarai » Ubangiji ya faranta kwanakinku bisa zagayowar ranar haihu war Assayada Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta
- Labarai » Munasabar tunawa da nasarar juyin juya halin muslunci a cikin Iran
- Labarai » Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
- Labarai » Shahadar Fatima Azzahra A.S
- Labarai » Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
Labarun da ba tsammani
- Labarai » Ubangiji ya gwabunta ladanmu da naku da tunawa da ranar shahadar kofar biyan bukatu imam musa alkazim(as).
- Labarai » Muhadara cikin hubbaren sayyada Fatima ma’asuma gameda munasabar zagayowar ranar haihuwar manzon Allah (s.a.w) hijira nada shekaru 1439.
- munasabobi » Takwas ga watan Shawwal tunawa da ranar da Wahabiyawa suka ruguje kaburburan A’imma (a’s)
- Labarai » SABUWAR SHEKARAR MUSLUNCI 1441 TARE DA DAWOWA KARATU DAGA RANAR ASABAR 14 GA WATAN MUHARRAM
- Labarai » Muhadarorin watan Ramadan Assayid Adil-Alawi
- Labarai » Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
- Labarai » Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
- Labarai » Taron sada zumunci
- munasabobi » Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Aliyu bn Muhammad Hadi aminicnin Allah ya kara tabbata a gareshi
- Labarai » Sayyid Adil-Alawi ya ziyarci cibiyar harkokin addini a garin Samarra mai tsarki
- Labarai » Darasi da ga rayuwar imam jawad
- Labarai » Muna taya daukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar shugabanmu maulanmu aliyu ibn Muhammad hadi annakiyu amincin Allah ya tabbata gareshi
- Labarai » muna taya gurguzun al’ummar musulmi murnar zagayiwar ranar haihuwar Sarkin Muminai Aliyu BN Abu Talib amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
- Labarai » Daga cikin muhimman darajojin da Fatima (as) ta kebantu da su
Labarai wanda akafi karantawa
- munasabobi » Ma'asumiyya Haura'u Zainab amincin Allah ya kara tabbata gare ta tare da Alkamin-samahatus sayyid Adil Alawi
- Labarai » Imam mahadi(af) da tsawon rayuwa a binciken sabuwar mahanga-tareda alkalamin sayyid adil alawi
- Sanarwa » Bude Bajakoli na litatafai na duniya karo na bakwai
- Labarai » Litatafan da aka buga
- Labarai » Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar haihuwar imam mai tausayi sarki aliyu ibn musa arrida amincin Allah ya tabbata gare shi
- Labarai » juyayin wafatin sayyida zainab Alkubra
- Labarai » Sirri daga sirrikan manzon Allah tsira da amicin Allah su kara tabbata gare shi da iyalansa-tare da alkalamin samahatus sayyid Adil-Alawi (dz)
- munasabobi » Soyayyar Husaini (as)ta haukatar da ni
- Labarai » Sayyid Adil Alawi ya halarci wurin karatun Al’qurani
- Labarai » jan hankali ko fadakarwa ga masu wa'azi
- Labarai » SIRRIN RANAR ASHURA
- Labarai » Sakon ta'aziyya
- Labarai » An wallafa mujallar kazimain me lamba 204/205 na watan rajab da shaaban na shekaran 1437H wanda yayi dai dai da shekaran 2016
- Lacca » Fatima zahara madubin kyawun Allah girmansa ya girmama
- Labarai » Ubangiji ya gwabunta ladanmu da naku da tunawa da ranar shahadar kofar biyan bukatu imam musa alkazim(as).
soyayyar husaini ta haukata ni-
Soyayyar Husaini
(as)ta haukatar da ni
Allah girmansa ya girmama, haka na kasantuwa da tattakin ma’arifa ta
hakika ya zuwa haramin gaibu mai buya wanda haskensa ya bayyana cikin
kawazazzabon dafufi cikin ranar Ashura ranar shahada, wajen soyayyar Allah ta
yi tajalli cikin duniyoyin mulki da malakutiyya cikin kausul nuzuli da su’ud,
hakika maganganu da ra’ayoyin Arifai da masu wusuli sun sassaba cikin tsanukan
sadarwa da taguwa wadanda da su mutum zai nade dukkanin masaukan Ahlin ma’arifa
da sairi da suluki, cikinsu akwai wanda ya tafi kan hikima, cikinsu akwai wanda
ya tafi kan ibada kamar salla azumi, an ce: Azkaru da tsoran Allah, wasu kuma
da tunani kan girman mahalicci da halitta, da tafiya daga halitta ya zuwa
gaskiya da gaskiya, daga gaskiya kan halitta da gaskiya, ance har kwakwale suka
gigita cikin mamaki da rudewa, zukatan da suke cikin kiraje sun
kekkece daga tsinkaya da afkuwa kan hanya madaidaiciya da siradi mikakke da
tafarki na hakika da kaiwa ga ya zuwa hakika tabbatattun abubuwa da
gaibun gaibobi.
Sai dai cewa hasken zuciyar mumini wanda shi daga shimfidadden hasken Allah da yake cikinsa yake yana shiryar da shi zuwa ga cewa lallai dukkanin hanyoyi zuwa ga Allah matsarkaki da sairin masaukan masu tafiya zuwa ga Allah mai girma da daukaka da dukkanin abin da ake ambato daga guzuri da taguwa daga abinda zai sadar da bawa zuwa ga ganawa da maulansa masoyinsa lallai suna daga cikin hanyoyi zuwa ga Allah lallai su hanyoyi sun haura adadin numfashin halittu sai dai cewa mafi kusancin hanyoyi zuwa ga Allah mafi alhrin guzuri da tsani falalar farko da karshe, haske mafi cika hanya mafi daidaita ga nade masaukai, kadai yana bayyanuwa cikin soyayya ga shugaban shahidai Husaini da Imam Ali ibn Husaini amincin Allah ya kara tabbata gare su, lallai soyayyarsa da kaunarsa kadai dai sun kasance madarar soyayyar Allah da soyayyar manzonsa
(حسين منّي وأنا من الحسين)
Husaini daga gare ni yake ni ma daga Husaini na ke.
Shi ne mafificiyar ibada mafificin wurudi da zikiri da aiki don kaiwa ga samuwa mai hukuntawa da cire hijabai masu katangewa zuwa ga kaiwa ga Allah matsaraki madaukaki, shi taimakon Allah ne ga wanda ya bi hanyar hakikanin gaskiya cikin shari’a da darika, hujja ne ta hankali, hasken zuciya ne, lallai da soyayyar Husaini hannun gaibun Allah da taimakonsa ke mikuwa da taimakon ubangiji madaukaki, da ludufinsa da jalabinsa boyayye hanyoyi ke haskaka zuwa ga ubagijin talikai.
duk mai son alherin duniya da lahira da farin cikin duniya da na lahira da sairi da suluki da wusuli ya zuwa ga Allah matsarkaki tsakanin zira’i ko mafi kusa daga haka cikin matsugunin gaskiya wajen sarki mai ikon yi, sai ya haskaku da fitilar shiriya Husaini, ya hau jirgin tsira na Husaini, lallai an rubuta kan Al’arshin Allah da koren launi wanda shi ne launin ma’arifa
(الحسين مصباح هدىً وسفينة النجاة)،
Husaini fitilar shiriya jirgin tsira.
Saboda haka ya rataya da direban jirgi a ruhance da jikance wanda shi ne Imam Husaini amincin Allah ya kara tabbata gare shi, duk wanda yake so ya kasance `yantacce cikin farin ciki duniya da lahira to ya yi riko da baban yantattu abin koyi ga rabautattu, shugaban mafiya alheri.
Ya zama dole da farko gabanin komai ya fara dandanar kaunar Husaini, lallai kauna ita ce wuce gona da iri wadda take mai kyawu cikin soyayya da tsanantawa wanda yake shi karkatar zuciya ne zuwa ga dadadda mai dadi, ma’ana mai dadi mafi dadada daga hakikar Husaini wacce ta yi tajalli ranar Ashura cikin ziyarar Ashura, duk sanda dadi yafi karfafa da cika cikin dadada sai soyayya da karkata su zama mafi girmama da girma har ya kai ga haddin wuce gona da iri, sai a kira shi da kauna ta hakika idan abin da ya ratayu da shi ya kasance daga Allah girmansa ya girmama, da abin da sunan Allah ya kasance kansa.
(اللّهم ارزقني حبّك وحبّ من يحبّك وحبّ كل عمل يوصلني إلى قربك)([1]).
Ya Allah ka azurta ni soyayyarka da soyayyar wanda yake sonka da son dukkanin wani aiki da zai sadar dani zuwa kusantarka.
Waken kauna na shugaban shahidai cikin kaunar Allah, ashe ba shi ne wanda ya fadi abin da aka danganta shi zuwa gare shi ranar Ashura ba:
تركتُ
الخلق طرّاً في هواكا |
|
وأيتمتُ
العيال لكي أراكا |
فلو
قطّعتني في الحبّ إرباً |
|
لما مَال الفؤاد إلی سواک
|
Kauna da soyayya na wuce gona da iri idan abin da ya ratayu da shi wanin Allah ne to zai zama abin zargi. Kamar yadda Imam Sadik amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya fada cikin soyayya da ba ta hakika ba
(قلوب خَلَت عن حبّ الله فأذاقها الله حبّ غيره)
Wasu zuciyoyi sun wofinta ga barin son Allah sai Allah ya dandana musu son waninsa.
Amma cikin soyayyar hakika da ratyuwar zuciya da Allah to babu wani batun wuce gona da iri, saboda abin da soyayyar ta ratayu da shi shi ne samuwa mudlaka cikin zatinsa da siffarsa da ayyukansa, shi ne kamala da kyawu tsantsa, babu karshe ga soyayyarsa hatta ma taken wuce gona da iri ya bijiro, duk wanda ya yi riko da igiyar shugaban shahidai amincin Allah ya kara tabbata gare shi cikin tafiyarsa da sulukinsa ya dandani soyayya da ma’arifa boyayya da ma’anoninta da misdakanta cikin zuciyarsa da samuwarsa, ya jikkanta ta cikin hakikarsa ta waje cikin rayuwarsa to hakika ya shiga mafi kusancin hanyoyi, mafi falalar guzuri zuwa ga Allah matsarkaki madaukaki.
Saboda Imam Husaini cikin zabinsa ga shahada da musiba mafi girma cikin ranar Ashura cikin kasar karbala, ya zabi hanya wacce Allah ya zanata ya ayyana masa cikin shafin samuwa cikin duniyar mulk da malakutiyya da gaibu da bayyane, karkashin soyayyarsa da fana’insa cikin Allah da wanzuwa tare da shi, shi ya cika cikin soyayya, kamar yadda ya zo cikin ziyara Jami’a Kabira
(والتّاميّن في محبّة اله)
Da cikakku cikin soyayya Allah.
Domin lallai ita soyayya tana daga mafhumin kulli mushakkak ma’abocin martabobi uliya da ardiyya, daga abin da bai kidaituwa basu iyakantuwa, cikin cancanta da tsanani da rauni da gabata da jinkirta, sai dai lallai shugaban shahidai Imam Husaini amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya jikkanta ma’ana ta hakika ga soyayyar Allah cikin waki’ar daffi mai radadi ranar Ashura goma ga watan muharram mai alfarma shekara 61 bayan hijra annabi, ta yadda sirrikan hakika da hakikani abubuwa da hakikanin Asraru suka bayyanu ranar Ashura a filin karbala, wannan yana daga cikin ma’anonin madaukakin hadisin annabi:
(إنّ لقتل الحسين في قلوب المؤمنين حرارة لن تُبرد أبداً) وكذلك (إنّ للحسين في بواطن المؤمنين معرفة مكتومة) ([2]).
(Lallai cikin kasha Husaini akwai wani zafafa cikin zukatan mumini da ba zai taba sanyaya ba har abada) haka ma (lallai Husaini yana da wata boyayyar ma’arifa cikin badinan muminai)
Farin ciki ga wana ya kasance ya sanni ya kaunace ni duk wana ya kaunace ni nima zan kaunace shi , sannan shi mai kauna yana dayanta cikin abin da yake kauna cikin ganin kyawunsa cikin idon zuciyarsa, sai ya ga masoyi abin kauna a halarce wajensa cikin zuciyarsa da badininsa, zuciya tafi tsananta riska daga basira da ido da gabban zahiri, daga nan ne kuma ma’anoni ke kewayawa wacce zuciya ta riske su kamar asraran Ashura da salladuwar haske kan ziyara da zuciya yafi girma daga kyawun dukkanin surorin zahiri wadanda ake riska, yafi dadada daga dukkanin dadin gaibu da bayyana, wannan ma’arifa boyayya wacce ta bayyanu cikin soyayya da kaunar Husaini, da son Husaini zaka kai ga son Allah ka ganshi da zuciyarka da tabbatattun imani ya gana da kai cikin sirrinka da hankalinka, ka sani ka fahimta da cewa mafi girma da daukaka dadi da mukamai., tukewar masaukai da sairi da suluki cikin sanin Allah shi ne soyayyarsa da son haduwa da shi da kallon tsarkin fuskarsa mai karamci.
Duk wanda ya ga girmansa da girmamarsa da kyawunsa da haskensa da tajallinsa cikin littafinsa da halittarsa, da girman jabarutinsa da malakutinsa cikin wadanda suka nufi zuwa gare shi da arifai, zai risketa cikin zurfin samuwarsa da zuciyarsa da hankalinsa, zai gansu da hasken idanun zuciya da halitta, a wannan lokaci zai watsi dadade-dadade da suke hana shi isuwa ga Allah
(واستتغفرك من كل لذة ليس فيه إسمك)([3]).
Ina neman gafararka daga dukkanin dadi da babu sunanka cikinsa.
Bai kusa ya yi tasiri kan wannan dadi ba wani dadin daban, sai dai cewa idan ya haramtu da ita da soyayyar duhu ko ta haske kamar hijabi mafi girma shi ne ilimin da bai cudanya da aiki, ya kasance daga haramtattu daga dadin son Allah da son wanda suke sonsa muhammadu da iyalansa amincin Allah ya kara tabbata gare su da soyayyar shugaban shahidai amincin Allah ya kara tabbata gare shi.
Soyayyar Allah ita ce magaryar tukewa da karkarewa mafi girma da arifai da makusanta, itace tsololuwa daukaka da salikai da masu tafiya zuwa ga Allah madaukaki, abin da ake ambata daga mukamai bayan soyayyar Allah kadai dai shi riba ce daga ribarsa kamar misalin shauki da debe haso, abin da zuciyarsa ke Ambato kadai dai shimfida ce daga shimfidu kamar zuhudu da hakuri, da soyayya samuwa ta bayyanu aka bayyanar da samamme, da soyayya mai ibada ya banbantu daga abin bauta, lallai shi ne tushen kowanne abu da rukunansa da hakikarsa kamar yadda ya zo cikin hadisi kudusi daga Allah matsarkaki wanda ya shahara cikn fadinsa:
(كنت كنزاً مخفيّاً فأحببتُ أن أُعرف فخلقت الخلق لكي أُعرف).
Na kasance taska boyayya sai na kaunaci da a sanni sai na halicci halitta domin a sanni.
Zukata da rayuka da tsarin halittarsu lafiyayya soyayyar kyawu da kamala mudlaka na jijiyantuwa cikinsu, dukkanin zuciya an halicce ta kan son mani’imcinta, mafi alherin abin da zai sadar damu zuwa ga soyayyar Allah mai ni’imtawa shine son Husain shi ne ya haukata ni…zahirinsa hauka badininsa tsantsar hankali…dukkanin godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai