sababun labare
- Labarai » Laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye cikin dandali sadar da zumunci na Instagram
- Labarai » Muhadarorin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Ramadan Mai albarka a shekara ta 1442 hijiri
- Labarai » Allah ya farantawa kwanakinmu da naku, muna farin cikin nuna murna da farin ciki ga al’umma musulmi shi’a da sunna kan haihuwar Imam Mahadi
- Labarai » MUNA TAYA KU MURNAR TUNAWA DA RANAR HAIHUWAR IMAM HUSAINI A.S
- Labarai » Allah ya faranta kwanakinku da namu cikin tunawa da ranar da aka aiko da Annabi
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar kofar samun biyan bukatu Imam Musa Alkazim (A.S)
- Labarai » muna taya gurguzun al’ummar musulmi murnar zagayiwar ranar haihuwar Sarkin Muminai Aliyu BN Abu Talib amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
- Labarai » Sabon littafi mai suna (Ruhul Inaba fi Tafsiril Du’a Sari’ul Ijaba) wallafar Samahatus Assayid Adil-Alawi
- Labarai » Ubangiji ya faranta kwanakinku bisa zagayowar ranar haihu war Assayada Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta
- Labarai » Munasabar tunawa da nasarar juyin juya halin muslunci a cikin Iran
- Labarai » Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
- Labarai » Shahadar Fatima Azzahra A.S
- Labarai » Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
Labarun da ba tsammani
- Labarai » Sayyid Adil-Alawi zai hau minbari don yin lacca kan Munasabar tunadawa rasuwar mawakin Ahlil-baiti Sayyid Muhammad Bakir Alawi
- Labarai » Muna ta’aziyya ga daukacin al’ummar musulmi bisa munasabar tunawa da wafatin sayyada Fatima `yar imam Musa Alkazim (as) wacce akewa alkunya da (ma’asuma) amincin Allah ya kara tabbata gare ta.
- Labarai » Muna taya ku murnar zagayowar shekarar haihuwar imam Rida (AS)
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa shahadar Imam Sajjad (a.s)
- Labarai » Labaran silsilar darussam akhlak na samahatus sayyid adil alawi a wanda zai kasance a jami’ar ahlil-baiti amincin Allah ya tabbata garesu.
- Labarai » Allah ya faranta kwanakinku da murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Aliyu Ibn Musa Arrida amincin Allah ya tabbata a gareshi.
- Labarai » Taron cibiyoyi masu da kula ziyarar arba’in
- Labarai » Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar shigowa uku ga watan Sha’aban Ranar da aka haifi Imam Husaini a.s
- Labarai » Godiya ga dukkanin wanda yayi tarayya cikin zaman makoki na shekara-shekara karo na 36 dangane da tunawa da wafatin Allah ya jikan rai Ayatullah Sayyid Ali Alawi.
- Labarai » Laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye cikin dandali sadar da zumunci na Instagram
- Labarai » Muna taya daukacin al’ummar musulmi ta’aziyyar tunawa da shahadar imam jawad (as)
- Labarai » HUBBAREN IMAM RIDA SUN GAYYACI ASSAYID ADIL-ALAWI LACCA
- Labarai » Sayyid Adil Alawi ya halarci wurin karatun Al’qurani
- Labarai » Muhadarar Samahatus Sayyid Adil-Alawi cikin hubbaren Sayyada Ma’asuma dangane da munasabar haihuwar Imam Mahadi amincin Allah ya tabbata gare shi
- munasabobi » BAYANI NA FARKO (1) BISA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAMAN SHEKARA 1441 H
Labarai wanda akafi karantawa
- munasabobi » Ma'asumiyya Haura'u Zainab amincin Allah ya kara tabbata gare ta tare da Alkamin-samahatus sayyid Adil Alawi
- Labarai » Imam mahadi(af) da tsawon rayuwa a binciken sabuwar mahanga-tareda alkalamin sayyid adil alawi
- Sanarwa » Bude Bajakoli na litatafai na duniya karo na bakwai
- Labarai » Litatafan da aka buga
- Labarai » juyayin wafatin sayyida zainab Alkubra
- Labarai » Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar haihuwar imam mai tausayi sarki aliyu ibn musa arrida amincin Allah ya tabbata gare shi
- Labarai » Sirri daga sirrikan manzon Allah tsira da amicin Allah su kara tabbata gare shi da iyalansa-tare da alkalamin samahatus sayyid Adil-Alawi (dz)
- munasabobi » Soyayyar Husaini (as)ta haukatar da ni
- Labarai » Sayyid Adil Alawi ya halarci wurin karatun Al’qurani
- Labarai » jan hankali ko fadakarwa ga masu wa'azi
- Labarai » SIRRIN RANAR ASHURA
- Labarai » Sakon ta'aziyya
- Labarai » An wallafa mujallar kazimain me lamba 204/205 na watan rajab da shaaban na shekaran 1437H wanda yayi dai dai da shekaran 2016
- Lacca » Fatima zahara madubin kyawun Allah girmansa ya girmama
- Labarai » Ubangiji ya gwabunta ladanmu da naku da tunawa da ranar shahadar kofar biyan bukatu imam musa alkazim(as).
Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Jafar bn Muhammad Sadik amincin Allah ya kara tabbata a garesu
An haifi imam Sadik (as) ranar litinin 27 ga watan Rabi’u Awwal shekara ta 83 da yin hijra wanda ya yi daidai da ranar aka haifi manzon Allah (s.a.w) hadisi ya zo daga manzon Allah (s.a.w) ya ce: Idan aka haifi `dana Jafar bn Muhammad bn Aliyu bn Husaini to ku kira shi da Assadik, daga littafin Muntahal Amal Shaik Abbas Qummi jz 2 sh 159
Imam Sadik (as) ya kasance mafi girmamar mutum a zamanin sa hakika ya assasa babbar makarantar fikhu cikin tarihi, dubun-dubatar dalibai sun kwankwadi ilimi a makarantar sa misaliin Sufyanul Sauri, Abu Hanifa, Malik bn Anas, Jabir bn Hayyan da wasun su, a daidai wannan lokaci Imam Sadik (as) ya kasance yana fuskantar kuntatawa daga hukumar Abbasiyawa daga fuskar Sarki Mansur Addawaniki Abbasim ya gaza jurewa girmamawar da mutane suke yi wea Imam Sadik (as) hakika ya kai shekaru 65, tarihi ya shaida cewa sau bakwai ana kirawo fada da aika masa da sammaci, daya daga cikin lokutan Muhammad bn Rabi’u yana cewa: babana ya kira ni hakika na kasance mafi kekashewar zuciya cikin `ya`yansa, sai ya ce mini: jeka gidna Jafar bn Muhammad take ka taho da shi ka kawo shi aduk halin halin d ayake ciki kada ka sake ka barshi ya canja wani abu daga wanda yake sanye da shi, sai Muhammad ya ce: sai na fuskanci gidan na sanya tsani na haura katangar gidan na hsiga sai na Jafar cikin wurin da yake sallah yana mai fuskantar Alkibla, bayan idar da sallar sa, sai nace masa ka amsa kiran Sarkin muminai sai ya ce: bara in canja tufafina, sai nace: ba zai yiwu ba, haka nan na fito da shi babu takalmi a kafafun sa kuma ba tare da rawani ba da cikakkun tufafi, a wannan lokaci shekarun sa sun tunkari 70, Muhammad ya ce: sai muka danyi tafiya a kasa sai Jafar ya gaji da tafiya jikinsa ya raunana sai na dora shi kan alfadari muka tafi sai kawai ga Rabi’u yana tsaye yana jiran zuwan mu shi kuma Mansur yana kira yana cewa ya Rabi’u ina Jafar bn Muhammad? Sa’ilin da Rabi’u ya ga Imam sai ya tarfe shi ya ce: ya `dan Manzon Allah banji dadin ganin ka cikin wannan hali sai dai cewa ya na iya an riga an bani umarni ne, sai Imam Sadik (as) ya ce: ka bar ni in yi sallah raka’a biyu, sai ya ce: yi sallarka ya `dan manzon Allah, sai yayi sallah raka’a biyu ya yi addu’arsa sannan Rabi’u ya rike shi da hannun say a shigar da shi wajen Mansur daidai wannan lokacin shi dagutun yana zaune kan karagarsa shi kuma Imam Sadik (as) yana tsaye gaban sa ba bu takalmi babu rawani sai Mansur ya ce masa cikin abinda ya gaya masa: shin yanzu baka jin kunya ya Jafar daga wannan gemanyar taka ace kana fadin karya kana raba kawukan musulmi?
Sai Imam Sadik (as) ya ce: ban aikata haka bay a sarkin muminai, sia Mansur ya ce: wadannan rubuce-rubucenka ne zuwa ga mutanen Kurasan kan kiransu zuwa ga bai’arka da tauye bai’ata, sai Imam (as) ya ce: wannan ba rubutuna bane ba zane ba ne ba kuma hatimi na bane lallai ni ban aikata haka ba a zamanin mulkin Banu Umayya wanda suka kasance mafi tsananin kiyayya garemu da gareku, ta kaka zan aikata haka a zamanin ku alhalin kune mafi kusanci da zumunci damu? A wannan ganawa Mansur ya dinga zare takobin sa yana maidata kubenta lokaci zuwa lokaci, sai ya sunkuyar da kansa daga baya ya dago shi ya ce: ya Jafar ina zatonka mai gaskiya sannan ya jawo Imam kusa da shi ya zaunar da shi a gefansa ya karrama shi ya sallame shi ya tafi, bayan tafiyar sa sai aka tambayi Mansur: me yasa ka dinga zare takobinka ka ne mayar da ita?sai ya ce: duk sanda na yi niyyar kashe shi sai naga manzon Allah (s.a.w) a gabana yana nannade hannun rigarsa yana shiga tsakani na da Jafar bn Muhammad, daga karshe da zare baki dayar takobina sai Annabi cikin halin fushi fuskar sa tati jajawur ya kusanto ni ya kusa ya damke ni sai na tsorata na janye niyya da nayi ka kashe shi.
An rawaito daga Muhammad Iskandari: a wani dare na shiga wurin Mansur Addawaniki sai na same shi a zaune kan shimfidarsa kyandir din fitila rarrataye a gabansa ya numfashi sanyayyen numfashi d ayake nuna cewa yana cikin wata damuwa. Sai ya ce: sai nace masa: ya sarkin muminai tunanin me kake haka? Sai ya ce: ya Muhammad lallai ni na kasance na kashe fiye da mutum dubu daga zuriyar Ali da Fatima amma shugaban su yana nan kuma shi ne jagoran su wato Jafar bn Muhammad, lallai na dau azama da niyyar kashe shi, sai ya ce: sai na ce masa: ya sarkin muminai lallai Jafar bn Muhammad mutum ne d aya shagaltu da ibada daga neman mulki sai ya ce: na san da haka ya Muhammad lallai kai ma kana Imani da imamancin sa da cewa shi imamin wannan al’umma ne sai dai cewa shi mulki guba ne, Mansur tsinannen Allah ya yi gangancin kashe Imam da amfani da mummunar dabara, hakika ya aikawa gwamnan Madinatul Munawwara da uamrnin ya cusa guba ga Imam Sadik (as) sai ya sanya guba cikin abincin sa, Imam Sadik (as) ya rayu bayan wannan guba tsakanin kwana daya zuwa biyu yana ta fama da radadin gubar har zuwan lokacin da wafati ya hallara gareshi cikin 25 ga watan Shawwal shekara ta 148 da hijira, `dansa Imam Musa Alkazim (as) ya hallara wajensa babansa Sadik (as) yayi masa wasiyya da wasiyyoyi daga cikin abinda yayi masa wasiyya ya ce: ya `dana ka kunna fitila kusa da jikina bayan ka binne ni lallai idna ruhi ya bar gangar jiki tana koma ainahin mahallinta idna ta ganshi cikin duhu sai ta gigice, sannan Imam Sadik (as) yayi sallama ya ce ga garinku nan ya koma ga ubangijinsa cikin halin fama da radadin gubar d aaka shayar da shi abin zalunta, an binne shi kusa da babansa Muhammad bn Aliyu Albakir (as) a makabartar Baki’a a Madina, ranar wafatin Imam (as) ta kasance ta kasance ranar da babu abinda kake ji a birnin madina sai sautin kuka da jimami rashinsa, yayin da aka fito da gawar sa sai wani mawaki ya fuskanto ya raira waka yana fadin:
Ina fadi alhali sun tafi da shi suna dauke da makararsa kan kafadunsu* shin wai kun san ma kuwa wane ne kuke dake da shi
Zaku kai
shi kushewa….. kamar misalin cikakken
wata da ya durkuso daga tsololuwar madaukakin wuri* an wayi gari masu zuba kasa
suna zuba kasa saman kabarinsa.
Imamin
mu (as) ya kasance abin buga misali cikin tsantseni da kyawawan dabi’u ta kai
ga hatta makiyan sa da suka kashe shi sai da suka yi kuka kan jimamin mutuwar
sa, hakika an rawaito cewa sa’ilin da ya bar duniya hatta Mansur Addawaniki la’ananne
sai da yayi kuka
wasu ba’arin su sun ce: na shiga
wurin Mansur sai na ga wasika a hannunsa yana karanta shi yayinda ya ganni sai
yayi wurgi da littafin zuwa gareni yana kuka yana cewa: wannan wasika ce daga
gwamnan mu na Madina yana bamu labarin wafatin Jafar bn Muhammad (as) a ina zamu samu misalin Jafar
bn Muhammad ?!